Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi ya rattaba hannu a kan kudirin dokar hukumar Hisbah ta jihar, inda ya kafa hukumar ta Hisbah a matsayin hukumar da za ta samar da ingantaccen tsarin zamantakewa da tarbiyya a jihar.
Wannan ci gaban ya zo ne kwanaki bayan majalisar dokokin jihar ta zartar da kudirin a zamanta na gaba daya, da nufin tallafa wa ayyukan hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa a fadin jihar.
Da yake jawabi jim kadan bayan rattaba hannu kan kudirin dokar, a wani karamin biki da aka gudanar a ranar Talata a zauren majalisar da ke gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar, yayin taron majalisar zartaswa na jiha na mako-mako, Namadi ya bayyana taron a matsayin wata gagarumar nasara, wacce ta nuna cewa sama da watanni takwas na kokarin kafa doka da mulki.
“A yau mun sanya hannu kan dokar Hisbah, wacce ta kafa hukumar Hisbah a matsayin hukuma a Jihar Jigawa,” in ji shi.
Gwamnan ya kara da cewa “Wannan tsari ne da aka fara watanni bakwai zuwa takwas da suka gabata, kuma yau cikin ikon Allah mun kammala shi”.
Namadi ya bayyana fatan cewa ayyukan hukumar ta Hisbah za su kawo kyakkyawan tsarin zamantakewa da tarbiyya a jihar.
Ya kuma bukaci jami’an Hisba da su gudanar da ayyukansu cikin tsoron Allah, adalci, da sadaukarwa.
Gwamnan ya kuma yaba wa ‘yan kwamitin kafa hukumar Hisbah bisa jajircewa, kwazon da suka yi, da sadaukarwa wajen gudanar da aikin da aka dora musu.
“Kokarin da suka yi ya taka rawar gani wajen ganin an aiwatar da kudurin,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Tare da sanya hannu kan wannan doka, a yanzu hukumar Hisbah ta samu cikakken ikon gudanar da ayyukanta a fadin Jihar Jigawa bisa aikinta na inganta kyawawan halaye, tabbatar da adalci ga al’umma, da kyautata rayuwar al’umma.
“Kafa Hisbah a matsayin hukuma babu shakka za ta inganta ayyukanta wajen inganta kyawawan dabi’u da adalci a cikin al’umma a jihar.
“Ana sa ran ayyukan hukumar za su yi tasiri mai kyau ga al’umma.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp