Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya soki magajinsa, Sanata Uba Sani, yana mai cewa ya koma mai makauniyya biyayya saboda goyon bayan da yake samu daga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
A shafinsa na Facebook, El-Rufai ya fara da wata magana mai cike da salo daga shahararren shirin talabijin na Burtaniya, Sherlock Holmes, kafin ya yi kaca-kaca da Gwamna Sani.
- Ko Ina Cikin Gwamnatin Tinubu, Zan Faɗa Wa APC Gaskiya – El-Rufai
- Kashi 85 Na Inibin Da Ake Nomawa Nijeriya, Daga Jihar Kaduna Ne – Dalhatu
Ya mayar da martani ne kan wata hira da Gwamnan Kaduna ya yi a gidan talabijin, inda ya yaba wa gwamnatin Tinubu tare da musanta wata ƙungiya da ke shirin kifar da gwamnati a zaɓen 2027.
El-Rufai ya ce wannan goyon baya da Gwamna Sani yake na da nasaba da sama da Naira biliyan 150 da Tinubu ya bai wa Kaduna a matsayin ‘biya, tallafi da gudunmawa’ a cikin watanni 18 da suka gabata.
El-Rufai, wanda ya rubuta da taken #ConcernedKadunaCitizen, ya ce: “Duk lokacin da na ga wannan gwamna yana magana da tsananin biyayya da rashin ‘yancin kai, sai in yi mamaki. Amma da na tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta bai wa Kaduna sama da biliyan 150 a cikin watanni 18 da suka gabata, sai komai ya zama a bayyane.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp