Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana farin cikinsa a lokacin da yake kaddamar da wata katafariyar tashar samar da iskar Gas (LNG da LCNG) wacce za ta fitar da tan 20,000 a kullum domin rabawa a fadin Nijeriya.
Da yake kaddamar da tashar a yankin Kakau, da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata, Gwamna Sani wanda ya samu wakilcin kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar, Ibrahim Hamza, ya ce, ya ji dadin halartar taron mai dimbin tarihi, inda ya kara da cewa, iskar gas na da amfani matuka wajen rage tsadar rayuwa da tattalin arziki sakamakon tashin farashin man fetur da kuma hauhawar farashin kayayyaki a kasuwannin duniya.
- Zaman Lafiya: MDD Ta Fara Yunkurin Samar Da Wani Sabon Tsari A Kaduna Da Katsina
- Gwamna Uba Sani Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Magajin Garin Zazzau
Kamfanin Greenville LNG ne ke jagorantar aikin wanda zai fitar da tan 20,000 kullum da za a rarraba a duk fadin kasar nan daga Kaduna.
Tun da farko, shugaban kuma babban jami’in GreenVille LNG, Mista Eddy Van Den Broeke, ya ce manufar kamfanin ya wuce magance karancin man fetur, inda ya kara da cewa, ta kunshi bayar da gudunmawa don samun ci gaba mai dorewa a Nijeriya. “Yayin da muke kaddamar da wannan tashar ta Kakau, muna kuma gayyatar ‘yan kasuwa da ke amfani da iskar gas a Kaduna su zo mu yi kasuwanci tare”. Broeke yace.