Kotun kolin Nijeriya ta sanya ranar Alhamis domin yanke hukunci kan karar da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi suka shigar na kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu wanda ya bayyana shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Daraktan yada labarai na kotun kolin, Dr Festus Akande ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
- Tirka-tirkan Takardun Tinubu: Ku Zo Mu Hada Hannu Don Fafutukar Wanzar Da Gaskiya – Atiku Ya Roki Obi, Kwankwaso
- Kotun Koli Ta Naɗa Alkalai 7 Da Za Su Saurari Daukaka Karar Atiku, Obi A Kan Tinubu
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai jam’iyyar PDP da LP suka shigar da kara a gaban kotun kolin.
A ranar 6 ga watan Satumba ne kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da karar da PDP da LP suka shigar gabanta kan rashin gamsashshiyar shaida, amma take Obi da Atiku suka daukaka kara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp