Gwamna Abba Yusuf ya buɗe Cibiyar Hadda da Nazarin Alƙur’ani, wadda aka raɗa wa suna Majidaɗi Institute for Qur’anic Research and Advancement (MIQRA).
An sadaukar da cibiyar ne ga mahaifin Kwankwaso, Musa Sale Kwankwaso. Kuma an gina cibiyar a gidan Kwankwaso da ke kan titin Miller Road, Kano.
- Nasihar Kwankwaso Ga Angwaye Da Amaren Kano: Ku Guji Binciken Wayoyin Junanku
- Shirin Bunƙasa Ilmi A Kano: Yadda Gwamnatin Abba Gida-gida Ta Tura Dalibai 1001 Karatu Kasashen Waje
Sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamnan Kano, Sanusi Bature ya fitar, ya ce, “Gwamna Abba ya yaba wa Sanata Rabi’u Kwankwaso dangane da wannan gagarimin tanadi da ya yi wa al’umma wajen bunƙasa ilmin addinin Musulunci.”
Gwamnan ya ce, an kafa cibiyar a daidai lokacin da ya dace, idan aka yi la’akari da yawan makarantun allo da na Islamiyya da ke faɗin jihar, waɗanda ke buƙatar a narkar da su cikin tsarin makarantun zamani, domin daƙile yadda almajirai ke ta gararamba kan tituna.
Gwamnan ya ƙara da cewa, Sanata Kwankwaso ya samu gagarimar nasarar ayyukan inganta rayuwar al’umma a lokacin mulkinsa, musamman wajen bunƙasa addinin Musulunci.
Ya bada misali da aikin katange dukkan maƙabartun cikin birnin Kano, gyaran masallatan Juma’a a faɗin jihar, gina makarantun Islamiyya a ƙananan hukumomi 44.
Sai dai kuma Abba ya nuna damuwa dangane da yadda Gwamnatin da ta shuɗe a Kano, ta ƙi ƙarasa sauran makarantun da Kwankwaso bai kammala ginawa kafin cikar wa’adin mulkin sa ba.
Saboda haka, Gwamna Abba ya yi alƙawarin ƙarasa makarantun, kuma ya bada umarni ga Ma’aikatar Ilmi ta fara tsare-tsaren fara ɗaukar ɗalibai domin fara zangon karatu.
Sanata Kwankwaso ya ce an kafa MIQRA domin ta riƙa horas da mahaddata Alƙur’ani maza da mata domin samun satifiket ɗin firamare da sakandare, ta yadda za su samu hanyar zarcewa makarantun gaba da sakandare da jami’o’i.
Ɗalibai daban-daban sun jinjina wa Kwankwaso da Gwamnan Kano dangane da wannan shiri mai albarka da aka gina.