A wata nasiha kuma gargaɗi da jan-kunne, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya shawarci ma’aurata 1,500 da aka ɗaura wa auren zawarawa a Kano cewa, kada su maida hankali wajen binciken wayoyin junansu.
Kwankwaso wanda shi ne madugun Kwankwasiyya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023, ya ce yawan binciken wayoyi da ma’aurata ke yi ne sahun gaba wajen yawan rabuwar aure.
- Zaben Kano: Ba Mu Yarda A Karya ‘Yancin Dimokuradiyya Ba – Kungiya
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 3 Bisa Zargin Fashi Da Makami A Jihar Kano
Kwankwaso ya yi wannan nasihar ce a ranar Juma’a, wurin walimar da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya wa Angwayen da Amaren a dandalin taro na Gidan Gwamnatin Kano, a ranar Asabar.
Tun da farko, a ranar Juma’a, Gwamna Abba Yusuf ne ya tsaya a matsayin waliyyin auren zawarawan, wanda aka gudanar lokaci ɗaya a faɗin ƙananan hukumomi 44 da ke Jihar Kano.
An shirya ɗaura aure 1,800 a lokaci ɗaya, amma kuma an samu ma’aurata 300 da lamarin bai yiwu ba, saboda dalilai na rashin lafiya.
“Na tabbata ana ta ba ku shawarwari daban-daban da nasihohi da gargaɗi kusan kila sau dubu. Malamai, iyaye da danginku da ma ‘yan kasuwa duk sun sha ba ku shawarwarin yadda za ku yi zaman aure a cikin kwanciyar hankali.
“To amma dai ni ina da wata shawara ɗaya, wato kada ku riƙa leƙe-leƙen binciken wayoyin junanku, domin yin hakan ya kawo sanadiyyar mutuwar aure da yawa,” inji Kwankwaso.
Daga nan ya yaba da irin namijin ƙoƙarin da Gwamnan Kano Abba Yusuf ya yi wajen shirya wannan gagarimin bikin auren dandazon zawarawa a Kano.
Haka kuma ya yaba wa Gwamnatin Kano dangane da kashe Naira miliyan 700 wajen ɗaukar nauyin ɗalibai 600 zuwa karatu jami’o’i daban-daban a ƙasashen waje.
A na sa jawabin, Gwamna Abba ya ce Gwamnatin Jihar Kano ce ta ɗauki nauyin shirya auren, ita ta biya sadakin kowane ango da kuma kayan ɗakin amarya, har da kayan gara na kayan abinci da kuma tallafin Naira 20,000 ga kowace amarya domin ta samu jarin fara sana’ar rage raɗaɗin tsadar rayuwa a gidajen auren su.
Daga nan ya hore su su yi zaman lafiya da juna a bisa tafarkin Musulunci.
Gwamna Abba ya ce, an zaɓo ma’auratan ne 30 daga kowace ƙaramar hukuma ɗaya, daga cikin ƙananan hukumomi 44 da jihar ke da su.
A jawabin sa, Shugaban Hukumar Hisbah, Aminu Daurawa, ya ce an ɗaura aure 1,500 a ranar Juma’a.
Ya ce waɗanda ba a samu damar ɗaura auren na su ba saboda lalurar rashin lafiya, su 264 ne, kuma za a ɗaura auren na su da zarar sun kammala shan magani nan gaba kaɗan.
Daurawa ya yi masu nasiha da su sa tsoron Allah a zamantakewar aure a tsakanin su.