Bayan shafe shekaru biyar cikin rashin tabbas da damuwar rayuwa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ceto dalibai 84 ‘yan asalin jihar da suka makale a kasar Cyprus, ta hanyar biyan bashin kudaden karatu da na masauki har Naira biliyan 2.24.
A wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnatin jihar ta tabbatar da biyan kudaden ga Jami’ar Near East da ke Cyprus, wanda hakan ya ba da damar daliban su karbi takardun kammala karatunsu da aka hana su na tsawon shekaru.
- Kotu Ta Yanke Wa Mutum 5 Hukuncin ÆŠaurin Wata 1 Saboda Awakinsu Sun Cinye Bishiyar Gwamnati A Kano
- Kotu Ta Soke Umarnin Kwace Filin Asibitin Tiamin, Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar ₦2.6bn
Wadannan daliban na cikin wadanda suka amfana da shirin tallafin karatu na kasashen waje da tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya kirkiro, amma gwamnatin da ta shude karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta dakatar da daukar nauyinsu.
Hakan ya jefa daliban cikin mawuyacin hali, inda aka kore su daga aji, aka fitar da su daga masauki, kuma suka fuskanci barazanar shari’a daga jami’ar Near East saboda rashin biyan kudaden da ake binsu.
A cewar sanarwar, cikin daliban da aka ceto akwai likitoci 28, da sauran wadanda suka karanta fannin aikin jiyya, da likitan hakori, da injiniya, kimiyyar kwamfuta, da aikin hada magani, da kimiyyar jiki. Gwamna Yusuf ya kuma ba da umarnin daukar su aiki kai tsaye a cikin gwamnatin Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp