Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rantsar da tsohon Sojan sama (Air Vice Marshal) Ibrahim Umaru a matsayin sabon Kwamishinan tsaro na cikin gida a yayin taron majalisar zartarwa na 28 a fadar gwamnati.
Tsohon hafsan Sojan saman, wanda ya yi ritaya, ya kasance Daraktan-Janar na sashin aiyuka na musamman a fadar gwamnatin jihar Kano kafin naÉ—in nasa.
- Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa
- Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci
Gwamnan Yusuf ya buƙaci sabon kwamishinan ya yi aiki da gaskiya, mutunci da himma wajen kare rayuka da dukiya a jihar, yana mai jaddada mahimmancin haɗin gwuiwa tsakanin hukumomin tsaro.
AVM Ibrahim Umaru mai ritaya ya na da gogewar shekaru da yawa a Sojan sama na Nijeriya (NAF) zuwa sabon muƙaminsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp