Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi sabbin naɗe naɗen muƙamai a gwamnatinsa.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya fitar da a sanarwar da ke bayyana cewa waɗanda aka naɗa sun haɗar da:
- Gwamnatin Kano Ta Yi Fatali Da Kudirin Sake Fasalin Dokar Haraji
- Dubun Wata Budurwa Da Wasu 5 Ya Cika Bayan Ta Sace Wayoyin Salula 30 Na Matan Aure A Kano
Hon. Ahmad Muhammad Speaker a matsayin mai bai wa gwamna shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Injiniya Ahmad a matsayin mai bai wa gwamna shawara kan Ayyuka, da malam Sani Abdullahi Tofa a matsayin mai bai wa gwamna shawara kan Harkokin Musamman.
Bugu da ƙari, Gwamnan ya naɗa Hon. Ibrahim Jibrin Fagge a matsayin shugaban hukumar kula da aiyukan ƙananan hukumomi da Hajiya Ladidi Ibrahim Garko a matsayin shugabar hukumar kula da ma’aikatan Jihar Kano.
An shirya gudanar da rantsarwa a ranar Litinin, 6 ga Janairu, 2025, a ɗakin taro na fadar gwamnati. Bikin zai haɗa da ƙaddamar da sabbin kwamishinoni da majalisar dokokin Kano ta tantance, tare da sabbin masu bai wa gwamna shawara.