Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya bukaci al’umma musamma masu kishin kasa a jihar su hada hannu da gwamnatisa wajen ciyar da jihar gaba.
Gwamna Radda ya yi wannan kira ne a jawabi da ya gabatar wajen wani biki na musamman da aka shirya domin karrama wani dan asalin jihar wanda ya kai matsayin farfesa na farko a tarihi a rundunar sojojin Nijeriya.
Gwamnan ya ba da tabbacin cewa kofarsa a bude take ga duka mai neman bayar da shawara a kan yadda za a ciyar da jihar gaba.
- Rashin Kishin Kasa Da ‘Yan Kasa A Kasafin Kudin Nijeriya Na 2024
- Rashin Kasuwa Da Cin Zarafi Na Cikin Manyan Kalubalen Kannywood – Sani Abubakar
Radda ya taya jami’i murna kan matsayin da ya samu na farfesa kan fasahar kirkire-kirkire. Ya ce matsyin da ya kai baban abin alfahari ne ga dukkan ‘yan asalin Jihar Katsina.
Ya yi fatan cewa mutanen jihar za su amfana daga basirarsa a matsayinsa na jami’in soja kuma mai kirkire-kire.
Da yake jawabi, Laftanar Kanal, Farfesa Abubakar Surajo Imam ya bayyana godiyarsa ga gwamnan jihar bisa karramawar da aka yi masa.
Ya tunatar da matasa a jihar su shiga cikin harkokin kananan kasuwanci don tallafa wa karatunsu. Ya ce hakan zai taimaka masu a duk inda suka tsinci kansu.