Gwamna Nasir Idris, ya bukaci maniyyata aikin hajjin bana daga jihar Kebbi da su kasance jakadu nagari a tsawon zaman da suka yi a kasar Saudiyya yayin da suke gabatar da aikin hajjin bana.
Dakta Nasir Idris, ya bayar da wannan shawarar ne a lokacin da ya kai ziyarar bankwana da rukunin farko na maniyyata a sansanin alhazai da ke Birnin Kebbi, ya bayyana cewa, an san alhazan jihar da zama masu bin doka da oda, inda ya yi kira gare su da su kiyaye irin wannan dabi’a.
Ya sanar da su cewa wannan shi ne karon farko da gwamnati mai ci ta shirya tsarin gudanar da aikin Hajji kuma ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin an gudanar da aikin jigilar mahajjata a filin jirgin sama na Sir Ahamadu da ke Birnin Kebbi amma hukumar ta aiyana cewa jirgin zai tashi ne a filin jirgin sama na Sakkwato.
Ya shawarci alhazai da su dauki irin wannan ci gaban a matsayin wani aiki na Allah inda ya ce shi ma zai yi aikin Hajjin bana tare da su don ba shi damar duba wuraren da ake bukatar gyara.
Gwamnan ya ba da tabbacin cewa an kammala duk wani shiri na jin dadi da jin dadin alhazai a kasar Saudiyya, sai dai ana jiran isowarsu kasa mai tsarki. Haka kuma ya bukaci mahajjatan da su kara himma wajen yi wa shugabannin kasa addu’ar samun nasara tare da samun zaman lafiya da ci gaba a Nijeriya.
A nasa jawabin, Amirul Hajj na jihar Kebbi na bana, tsohon ministan harkokin cikin gida, Janar Muhammadu Magoro, ya shaida wa gwamnan cewa an samar da komai domin ganin an gudanar da aikin Hajji cikin sauki.
Janar Magoro ya sanar da cewa likitoci goma sha takwas da adadin ma’aikatan lafiya da suka dace za su raka maniyyatan zuwa Saudiyya domin kulawa da bukatunsu na lafiya. Ya kuma kara da cewa an kafa kwamitoci goma sha hudu don tabbatar da jin dadin alhazai.
Matan Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris, Hajiya Zainab Nasir da Hajiya Nafisa Nasir sun bukaci maniyyata da su yi addu’a ga jihar da kasar Nijeriya yayin da suke a kasa mai tsarki.
A nata jawabin, Hajiya Zainab ta ce jerin laccoci da shirye-shiryen fadakarwa da karawa juna sani da aka yi wa mahajjata an yi su ne domin su tsara dabi’u da tunaninsu ta yadda za su fahimci mahimmanci da abubuwan da ke tattare da aikin hajji.
Ta bayyana cewa gwamnati ta yi tanadin isassun wuraren kwana, tsarin ciyarwa, kayan aiki, tallafin magunguna da sauran kayan agaji da za su samu nasarar gudanar da aikin hajji.
A nata bangaren, Hajiya Nafisa, ta bukaci alhazai da su kula da kayansu, ta kuma shawarce su da su yi taka-tsan-tsan wajen yin musanyar kudade a lokacin zamansu a kasar Saudiyya.
“Ya kamata ku tabbatar kun bar darussan da aka koya daga shirye-shiryen fadakarwa da laccoci daban-daban su shafi halayenku da kyau yayin gabatar da addu’o’i ga jihar Kebbi da kasar Nijeriya baki daya,” in ji ta.
Da yake jawabi a madadin mahajjatan, Ahmad Galadima daga karamar hukumar Argungu ya godewa gwamnan bisa tsarin da ya dace na gudanar da aikin Hajji