Gwamnan Jihar kebbi, Dokta Nasir Idris Kauran Gwandu ya tabbatar da nadin Sanusi Mika’ilu Sami a Matsayin Sabon Sarkin Zuru, Wanda nadinsa ya biyo bayan rasuwar Sarkin Zuru, Alhaji Muhammad Sani Sami Gomo II, Wanda ya rasu a ranar 16 ga watan Agusta 2025 a wata Asibiti dake kasar London.
Sanarwar nadin sabon Sarkin na zuru, ya fito ne daga bakin Kwamishinan Ma’aikatar kananan Hukumomi da Masarautun gargajiya na jihar, Alhaji Abubakar Garba Dutsinmari a yammacin Alhamis a garin na zuru.
- Hukumar Shige Da Fice Ta Ƙara Kuɗin Fasfo Zuwa N100,000, N200,000
- Ƴansandan Libya Sun Kama Ƴan Nijeriya Biyu Kan Zargin Fashi
Kwamishinan ya ce” nadin Sanusi Mika’ilu Sami bisa ga sakamakon zaben da rahoton da kwamitin tantancewa da zaben sarki na masarautar ta zuru, inda kwamitin suka tantance mutane uku kan mukamin sabon Sarkin Zuru.
Acikin mutum ukun da aka tantance, Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami ya samu kuri’u mafi rinjaye a matsayin Wanda aka zabe shi ya zama sabon Sarkin Zuru. Bisa ga hakan ne Gwamnan Jihar ya sanya hannu kan nadin Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami a matsayin Sabon Sarkin Zuru.
Dutsinmari ya gabatar da takardar nadin sabon Sarkin ga Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami, inda ya taya shi murnar zama sabon Sarkin Zuru.
Haka kuma ya godewa Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu kan nada Sanusi Mika’ilu Sami a matsayin Sabon Sarkin Zuru.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp