Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya rantsar da Mai shari’a Umar Abubakar a matsayin babban mai shari’a da Mai shari’a Sadiq Usman Mukhtar a matsayin Grand khadi na jihar.
Mai shari’a Abubakar da mai Shari’a Mukhtar sun dauki rantsuwar kama aiki ne a gaban Gwamnan.
- Ta’addanci: NDLEA Ta Cafke Miyagun Kwayoyi Zuwa Dazukan Zamfara Da Kebbi
- Gwamna Nasir Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Naira Biliyan 250 Ga Majalisar Dokokin Kebbi
Bayan kammala rantsuwar ta su, Gwamna Nasir ya sanya hannu kan takardar rantsuwar don tabbatar da su akan sabbin mukamansu.
A wani labarin makamancin haka, gwamnan ya kuma kaddamar da shugabanni da mambobin kwamitin gudanarwa na manyan makarantun jihar guda biyar da kuma wasu sabbin shugabannin hukumomin guda uku da aka kafa.
Hukumomin da Gwamna Nasir Idris ya kaddamar sun hada da hukumar kula da harkokin kimiyya da fasaha ta Jami’ar jihar Kebbi Aliero, da kwalejin Ilimi ta Adamu Augie da ke Argungu da kuma kwalejin koyon aikin jinya da ke Birnin Kebbi.
Sauran sun hada da kwalejin kimiyya da fasaha ta kiwon lafiya da ke a Jega da kuma kwalejin share fage da ci gaba da karatuttukan hukumar Yauri.
A nasa jawabin, Gwamna Nasir Idris ya ce duk wannan nadi an yi shi ne bisa cancanta da kwarewa da suke da ita a fannoninsu.
Don haka ina kira gare ku da ku yi aiki tukuru wajen ganin an samar da ci gaba ga wannan cibiyoyi da hukumomin da aka baku shugabanci.