Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya rantsar da sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomi da mataimakansu a wani biki da aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Birnin Kebbi. Babban Jojin jihar, Mai shari’a Umar Abubakar, ya bawai Sabbin Shugabanni rantsuwar kama aiki.
A nasa jawabin, Gwamna Nasir ya bayyana farin cikinsa kan nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaben kananan hukumomi 21 da aka gudanar a fadin kananan hukumomin 21 a ranar 31 ga watan Agusta, 2024, da KESIEC ta gudanar. Haka kuma ya alakanta wannan nasara da irin nasarorin da ya samu wajen jagorancinsa, ya kuma yi kira ga shuwagabannin da su fara gudanar da ayyukan raya kasa da al’ummar mazabarsu za su amfana da shi.
- Hamas: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Isra’ila Saboda Ƙin Amincewar Ƙasar Kan Tsagaita Buɗe Wuta
- Bola Tinubu Da Wasu Shugabannin Afirka Sun Iso Beijing Don Halartar Taron FOCAC
Gwamna dai ya jaddada tsarin tafiyar da gwamnati, inda ya bukace su da su ci gaba da tafiyar da kowa tare da tabbatar cewa sun gudanar da mulkin da jama’ar yankunan kananan hukumominsu ke bukata.
Hakazalika, gargadi shugabannin da su ji tsoron Allah yayin gudanar da ayyukansu a kananan Hukumomin su.
Da yake jawabi a madadin sabbin shugabannin da aka rantsar, Hon. Dahiru Nayaya Ambursa, Shugaban karamar hukumar Birnin Kebbi sun yi alkawarin bayar da goyon baya da kuma biyayya ga Gwamnan, tare da yin alkawarin samar da ci gaba a kananan hukumominsu. Ya taya Gwamnan murnar nasarar lashe zaben tare da gode masa da ya same su sun cancanci tsayawa takara a kananan Hukumomin su.