ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Za Ta Ƙarfafa Alaƙa Da Indonesiya A Taron Ƙasar Da  Ƙasashen Afirka Karo Na Biyu

by Sulaiman
2 years ago
Indonesiya

Gwamnatin Nijeriya za ta ƙarfafa hulɗar da ke tsakanin ta da Indonesiya yayin da aka fara taron ƙasar da nahiyar Afirka karo na biyu a birnin Bali na ƙasar Indonesiya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan, wanda yanzu haka yake Indonesiya domin wakiltar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban Tawagar Nijeriya a taron.

ADVERTISEMENT
  • ACF Ta Yaba Wa Tinubu Kan Amincewa Da Ziyarar Sulhu Da Shugaban Sojojin Nijeriya Ya Kai A Nijar 
  • Masanin Habasha: Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Jure Sauye Sauye Cikin Tsawon Lokaci

Taron zai gudana ne daga ranar 1 zuwa 3 ga Satumba, 2024.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Taken taron, “Bandung Spirit for Africa’s Agenda 2023” kwatankwacin taron Asiya da Afirka ne mai tarihi na 1955 da aka fi sani da “Taron Bandung”, wanda Indonesiya ta shirya, wanda ya nuna wani sabon babi na haɗin kai da haɗin gwiwa a cikin alakar da ke tsakanin nahiyoyin biyu.

Taken, kuma yana da nufin zurfafa haɗin gwiwa tsakanin Muradin Indonesiya na 2045 da Ajandar Tarayyar Afirka ta 2063.

Nijeriya da Indonesiya dai suna da alaƙa mai ƙarfi tsawon shekaru, wanda tun a shekarar 2022 gwamnatin Indonesiya ta ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da za ta zuba jari a cikin ta a nahiyar Afirka, matakin da ke nuna amincewar ƙasar da ƙarfin tattalin arzikin Nijeriya.

Adadin cinikayyar da ke tsakanin ƙasashen biyu ya kai dala biliyan 6 a 2023, wanda ya ƙaru daga dala biliyan 4 shekaru goma da suka gabata.

Bugu da ƙari, tallafin da Indonesiya ta bai wa Nijeriya ya haɗa da ba da gudunmawa a 2023 ta allurar rigakafi ta Pentavalent miliyan 1.58, wadda darajar ta ta kai kusan dalar Amurka miliyan 2, wanda ya kasance muhimmi wajen kare yaran Nijeriya daga cututtuka masu barazana ga rayuwa.

Yayin da yake Indonesiya, Minista Idris zai bayyana damarmakin saka hannun jari a Nijeriya a ɓangarori daban-daban da kuma bayyana nasarorin da aka samu na zamantakewa da tattalin arziki na Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Tinubu.

Zai kuma nemi a bai wa ‘yan kasuwa na Nijeriya damarmakin da za su shiga cikin tattalin arzikin Indonesiya.

“Ina fatan in wakilci Mai Girma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnati da al’ummar Nijeriya a taron Indonesiya da Afirka karo na biyu, da kuma taron da zai zama wani muhimmin abin tunawa a cikin tafiyar ƙarfafa alaƙa tsakanin Indonesiya a ɓangare ɗaya da Nijeriya da Afirka a ɗaya ɓangaren,” inji Idris.

Indonesiya
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

MASU ALAKA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Next Post
Sojoji Sun Kama Masu Safarar Makamai Ga Ƴan Ta’adda

Sojoji Sun Kama Masu Safarar Makamai Ga Ƴan Ta'adda

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.