Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya shawarci al’ummar jihar da suke da niyyar yin tafiya domin sauke farali zuwa kasa mai tsarki a shekarar 2025 da su tabbatar su na cikin koshin lafiya kafin fara tafiya zuwa Saudiyya.
Gwamnan ya nemi al’umma jihar da su ci gaba da godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya raya mu zuwa yanzu kuma ya kawo ci gaba da bai wa al’umma yalwar rayuwa har aka samu gudanar da ibadar azumin watan Ramadana.
Da yake magana a ranar Talata kan bukukuwan Sallar karamar ta bana da aka shirya domin yin godiya na musamman ga Allah da ya gudana a Lagos House, Marina.
“Zuwa watan Mayu, maniyyata za su fara tafiya zuwa kasar Saudiyya. Don Allah ku tabbatar kuna da cikin koshin lafiya.
“Idan ba ka da lafiya, ka hakura da tafiyar aikin hajji a 2025, ka zauna abunka ka yi addu’a daga nan gida Nijeriya,” ya tsawarta.
Gwamnan ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan tare da addu’ar Allah ya karvi ibadu.
“Ina addu’ar Allah ya ci gaba da ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da hadin kai a tsakani. Za mu ci gaba da shaidar bukukuwan Sallar.
“Ina kuma gode wa shugabannn addininmu bisa koyar da mu alkur’ani mai girma. Ina fatan wasu shekarun za su samemu cikin kwanciyar hankali,” Sanwo-Olu ya shaida.
Ita kuma a nata vangaren, matar gwamnan jihar, Dakta Ibijoke Sanwo-Olu, ta nuna farin cikinta kan yadda ake gudanar da shagulan salla a jihar cikin kwanciyar hankali tare da yin kira ga mutanen Legas da su ci gaba da nuna soyayya da kauna ga wadanda ba su da karfi da marasa galihu ta hanyar musu kyautuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp