ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (1)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
11 months ago
Hijira

Auzu billahi minash shaidanir rajim, bismillahir rahmanir Rahim. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim.

Masu karatu barkanmu da sake haduwa a wannan makon cikin filinmu na Dausayin Musulunci.

  • Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (3)
  • Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)

Mun gode Allah, a makon da ya gabata mun kammala bayani a kan falalar ziyarar Kabarin Annabi (SAW). Abin da ya samu Allah ya amfanar da al’ummar Annabi (SAW) da shi.

ADVERTISEMENT

A yau kuma za mu shiga sabon karatu a kan sabuwar shekarar Hijirah wadda a bana ita ce ta 1447 kuma shekara ta musamman ga duk halitta saboda a cikin shekarar ce Manzon Allah (SAW) yake cika shekara 1500 da haihuwa.

Shi Musulmi kullum cikin ganin girman baiwar Allah yake, kullum a cikin kankan da kai yake a wurin Allah, cikin bautar Allah Tabaraka wa ta’ala. Don haka Allah yake ta jujjuya masa kwanaki da watanni da shekaru domin abin ya ba da sha’awa ya yi kyau. Kuma ya zamto kullum Musulmi ya sabunta himmarsa da tafiyarsa zuwa ga Allah. Yanzu mun gode Allah, mun yi karatuttuka game da Hajji, ga shi har an kammala Hajjin ma, mun gode Allah. Sannan ita kanta shekarar ma ta kare, mun shiga sabuwar shekara ta 1447 da yin Hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makkah zuwa Madina tare da kafa Daular Musulunci. Idan ka kawo shekara 53, sai lissafi ya zama shekara 1500 da haihuwar Annabi (SAW). Mun gode Allah.

LABARAI MASU NASABA

Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed

MURIC Ta Zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Da Fifita Kiristoci Fiye Da Musulmi

Lallai wannan kalanda ana ce mata ta Musulunci; gaskiya ne, ta Musulmi ce tsantsa sannan kuma ta duk halitta ce domi duk halitta suna amfani da wannan, ko sun sani ko ba su sani ba. Sai dai kawai, mu a cikin ibadojinmu Addininmu Balarabe ne kuma Larabawa da wata suke yin kirgensu, kuma shi ne ya dace da halittar Dan Adam, mun gode Allah.

Muna kira ga daukacin al’ummar Musulmi kowa ya yi tanadi na musamman kar ya bari a bar shi a baya, a bana idan Allah ya kai mu watan Rabi’ul Auwal maulidin da za a yi shi ne zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa.

Yadda abin yake shi ne, idan ka dauki shekarun haihuwar Manzon Allah (SAW) 40 kafin a fara aiko masa da manzanci ka hada da shekarun da ya yi a Makkah guda 13 bayan fara saukar da manzanci zai ba ka shekaru 53. To, idan ka hada shekaru 53 da shekarar Hijira 1446 a bara, lissafin zai ba ka cewa a baran Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1499 da haihuwa. A bana kuma zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa kenan.

Hatta wadanda ba su yin maulidi ya kamata a bana su yi kokari su yi wani abu ko yaya kar a bar su a baya, saboda yanzu idan Allah ya ja da rayuwarmu muka ga watan Rabi’ul Auwal mai zuwa lokacin da Manzon Allah zai cika shekara 1,500 da haihuwa, to zai yi wahala mu ga lokacin da zai cika shekara 2,000 kuma. Domin da wahala a samu wani daga cikin mutanen da ke rayuwa a doron kasa yanzu ya kara wasu shekaru 500 a raye.

A lokacin da Annabi Isah (AS) ya cika shekaru 2,000 da haihuwa an ga yadda duk duniya ta dauki murna, to mu ma ya kamata Musulmi mu girgiza duniya da bukukuwa na murnar mu ma Annabinmu (SAW) ya cika shekaru 1,500 a duniya. Wannan babban alheri ne da tarihi a rayuwarmu. Allah ya hore mana dukkan abun da za mu yi hidima da shi Albarkar Annabi (SAW).

Game da shiga sabuwar shekarar musulunci ta hijirah kuwa ta 1447 da muka shigo, za mu yi waiwaye game da tarihin kafuwar shekarar kamar yadda muka taba yi a baya saboda karatu ne mai muhimmancin gaske.

Annabi (SAW) ya umurce mu da mu bi sunnarsa, mu bi sunnar Khalifofi shiryayyu bayansa. Wannan Hijirah sunnar Manzon Allah (SAW) ce. Kuma sunnar Sayyidina Umar ce (RA) da sauran Sahabbai. Domin Sayyidina Umar ne ya kafa mana wannan kalandar ko in ce kirgen ta Hijirah.

Manzon Allah (SAW) ya yi Hijira ne a watan Rabi’ul Auwal, amma me ya sa ba a faro kirgen daga watan ba? Abin da suka yi na farowa daga Muharram akwai kaifin hankali a ciki. Akwai wata babbar hidima a cikin watan na Rabi’ul Auwal, ita ce murnar haihuwar Manzon Allah (SAW). Idan abu biyu ya zamo wuri daya sai daya ya kwace daya, kamar a ce yau ce ranar haihuwar Manzon Allah kuma yau ce ake bikin sabuwar shekarar Hijira, dole daya ya kwace daya. Bare wanda aka hada da shin ma Mauludi ne na Manzon Allah (SAW). To, shin waye ana bikin haihuwar Manzon Allah zai tuna ya yi wata murnar sabuwar shekara? Wannan ya sa suka dauko farawar sabuwar shekarar suka matso da ita baya ta fara a watan Muharram.

Sannan a halittar Allah, Allah ya shirya cewa wata guda 12 ne, idan wata ya fito ya koma a ce Muharram, idan ya fito ya yi girma har ya cika kuma ya fara karewa har ya tafi baki daya sai a ce Muharram ya kare, idan ya kuma fitowa sai a ce Safar. Watan da ya fito a Muharram shi din ne dai zai kara fitowa bayan karewarsa a Muharram din a ce Safar. Shi din ne dai yake ta wannan juyawar. To watan idan zai yi ta fitowa babu kayyadadden kirga, sai a yi ta kirgawa har zuwa miliyoyi. Shi ya sa Allah ya shirya cewa idan watan ya fito sai a ce daya, idan ya koma ya sake fitowa a ce biyu har dai a yi 12. Idan an yi haka sai a ce shekara ta kare, sai a kuma dawowa wata sabuwar shekara. To a wannan abu da Allah ya shirya, sai ya sanya Almuharram a matsayin farkon wata. La’alla Annabi Adamu (AS) yana da wani suna da yake kiran watan daban da na Larabawa ko kuma ya zama daya ne, ga shi nan dai Muharram shi ne farko.

Wanda aka gada wajen Larabawa dai Almuharram shi ne farko, sai Safar, Rabi’u Auwal, Rabi’u Akhiri, Jimada Auwal, Jimada Akhir, Rajab, Sha’aban, Ramadan, Shauwal, Zulkida sai kuma Zulhajji. Sauran wasu Yarukan ma suna da nasu, kamar Turawa suna da Janairu, Fabarairu, Maris har zuwa Disamba. Idan ka ce ai na turawan sunayen gumaka ne, to ai na Musuluncin ma ba sunayen Allah ne aka sa musu ba, kinaya ce. Kila an ambace su da yanayin da ake samu a lokacinsu. Kila kamar lokaci ya yi zafi akwai rana sosai sai a ambace shi da Ramadana, idan kuma Rajab ne kila lokacin da suke cire kan mashi ne saboda ba za a yi yaki ba, sai a ce masa Rajab. Ko wanne dai za ka ga kila saboda wani abu da yake faruwa lokacin aka ambaci watan da sunansa na wannan abun. To amma Annabi (SAW) lokacin Hajjinsa na karshe a cikin hudubarsa ya fadi cewa, “zamani ya kewaya ya kewayo”. Tun ranar da Allah ya halicce shi a Azal, aka fara da Muharram a farko, haka abin yake har zuwa 12. Sai dai, ko wane yaruka suna da nasu. Yanzu lokacin da wannan Muharram din ya shiga, ya kasance a farkon wata na 9 ne a wurinsu. Su dai suka kai shi na 9 mu babu ruwanmu, a wurin Allah dai Muharram shi ne na daya.

Don haka idan Musulunci zai yi kirge dole ya dawo Muharram, bai taba na Rumawa da sauransu ba saboda ba za su yarda ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa ba a sa Rabi’u Auwal a matsayin farkon watan shekarar Musulunci ba, da kuma kasancewar Rabi’ul Auwal shi ne na uku a watannin Musulunci, kuma ai ba za a fara kirge daga uku ba. Wannan ya sa Rabi’ul Auwal bai zama farkon shekara ba. Haka Allah ya shirya tun Azal. Haka Annabi (SAW) ya fada a ranar Hajjin ban-kwana cewa zamani ya kewaya ya kewayo. Ka ga yanzu, Allah ya ganar da Sahabbai abin da Annabi (SAW) ya koyar da su, kuma dama mutane ne Malamai, duk abin da Annabi (SAW) ya koyar da su suna yi a aikace.

Sannan me ya sa ba za mu dinga yin murnar shekarar ba a watan da aka yi Hijirar na Rabi’ul Auwal? Sai mu ce watan Rabi’ul Auwal yana da nashi gagarumin murnar da muke yi na bikin haihuwar Manzon Allah (SAW), shi kenan ka ga ba sai an rungumi wani biki na daban an sake kaiwa cikinsa ba. Kamar dai yadda aka samu sabani na ilimi a tsakanin Sayyidina Umar da Sayyidina Aliyu (RA). Domin sabanin malamai rahama ne ga al’umma.

Za mu tsaya a nan sai mako mai zuwa za mu ci gaba cikin yardar Allah. Allah ya kaimu da rai da lafiya Albarkar Annabi (SAW).

Hijira
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Komawa Ga Allah Ta Hanyar Yawaita Istigfari
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Bukatar Kula Da Tarihi A Musulunci
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Albishir Ga Iyayen Da Suka Karantar Da ‘Ya’yansu Alkur’ani (2)

MASU ALAKA

Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed
Siyasa

Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed

May 5, 2026
MURIC Ta Zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Da Fifita Kiristoci Fiye Da Musulmi
Addini

MURIC Ta Zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Da Fifita Kiristoci Fiye Da Musulmi

May 2, 2026
Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…
Addini

Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…

March 20, 2026
Next Post
Ba A Taɓa Nuno Bidiyon Shugaban Jam’iyyarmu Ta ADC Yana Cusa Dala A Aljihu Ba —Dalung

Ba A Taɓa Nuno Bidiyon Shugaban Jam'iyyarmu Ta ADC Yana Cusa Dala A Aljihu Ba —Dalung

LABARAI MASU NASABA

Atiku Ne Ya Fi Dacewa Da Tikitin Takara A ADC Amma Ya Kamata Ya Janye — Baba-Ahmed

2027: Kasancewa Ɗan Arewa Kaɗai Ba Zai Tabbatar Da Samun Ƙuri’u Ba – Baba-Ahmed

June 4, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.