ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za Mu Tabbatar Da Yin Aiki Da Ƙungiyar Mahaddata Alƙur’ani – Daurawa

by Abdullahi Muh'd Sheka
1 year ago
Daurawa

Babban kwamandan rundunar Hisba ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana aniyar hukumarsa ta yin aiki tare da sahihiyar kungiyar Mahaddata Alkur’ani ta ƙasa.

Shehin Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani na kasa, Goni Sunusi Abubakar wanda ya samu rakiyar shugaban kungiyar reshen Jihar Kano, Gwani Laminu Mahmud Salga suka kai masa ziyara a ofishinsa.

  • NDLEA Ta Kai Samame Fitattun Wuraren Shaye-shaye, Ta Cafke Mutane 19 A Kano
  • Wani Matashi Ya Ƙone Kansa A Kano Saboda Yana Son Zuwa Aljanna 

Da yake tsokaci kan korafin da shugaban ya gabatar cewar wani dan Hisba na yin sojan gona da sunan Majalisar Mahaddata Alkur’ani kan shi ne aka zaba a matsayin shugaban kungiyar Jihar Kano, Daurawa cewa mutumin ya zo da takardar cewa shi ne shugaban kungiyar na Jihar Kano, wanda kuma ya bukaci a sa masa albarka.

ADVERTISEMENT

Don haka sai Daurawa ya tabbatar wa da shugabannin Majalisar Mahaddatan cewar za su gudanar da bincike, domin ba zai yi wu a ci gaba da irin wannan a hukumar ta Hisba ba, daga nan sai ya taya shugabannin majalisar murna tare da alkawarin yin aiki da sahihiyar kungiyar mahaddatan kamar yadda aka gani a lokacin rabon tallafin shinkafar da Gwamnatin Kano ta bayar.

Da yake gabatar da jawabinsa, shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani na kasa, Goni Sunusi Abubakar ya bayyana matukar damuwa bisa yadda wani mutum ke amfani da sunan wannan kungiya yake bayyana kansa a mtsayin shugaban kungiyar na Jihar Kano. 

LABARAI MASU NASABA

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed

A lokacin ziyarar, Sheikh Daurawa tare da alkalin kotun hukumar ta Hisba ne suka karbi tawagar shugaban majalisar mahaddatan na kasa, wanda ya samu rakiyar Gwani Laminu Mahmud Salga,  Gwani Imam Nazafi Abubakar  Gwani  Sabo Mai Rigar fata, Gwani Rabi’u Sulaiman Tarauni da Abdullahi Muhammad Sheka.

Daurawa
Abdullahi Muh'd Sheka
+ postsBio
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    Sakamakon Matsin Lambar Jami’an Tsaro, ‘Yan Ta’adda Na Fuskantar Ƙarancin Abinci
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    Kisan Gillar Mutum 7 A Kano: Sarakuna Da Malamai Da Iyaye Sun Nemi A Gaggauta Yanke Wa Waɗanda Ake Zargi Hukunci
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo

MASU ALAKA

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa
Ta’aziyya

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

August 2, 2026
Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed
Siyasa

Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed

May 5, 2026
MURIC Ta Zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Da Fifita Kiristoci Fiye Da Musulmi
Addini

MURIC Ta Zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Da Fifita Kiristoci Fiye Da Musulmi

May 2, 2026
Next Post
Minista Ya Yaba Wa Hafsoshin Soji Kan Cigaban Da Aka Samu A Fannin Tsaron Ƙasa

Minista Ya Yaba Wa Hafsoshin Soji Kan Cigaban Da Aka Samu A Fannin Tsaron Ƙasa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.