Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sakkwato ya aminta da bayar da kyautar goron Sallah ga baki ɗaya ma’aikatan jihar da na ƙananan hukumumi da masu karɓar fansho da masu karɓar alawus.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewar za a bayar da kyautar goron sallar ne a rukuni biyu, wato rukuni na farko wanda ya haɗa da ma’aikatan jiha da ƙananan hukumomi waɗanda za a ba su ₦30,000 kyauta.
- Gwamna Aliyu Ya Tsige Hakimai 15 Na Sokoto
- Dalilin Haramta Tafiyar Dare A Iyakokinmu Da Katsina Da Sokoto – Gwamnatin Zamfara
Rukuni na biyu, waɗanda za su amfana da kuɗaɗen ya ƙunshi masu karɓar fansho da masu karɓar alawus a ƙananan hukumomi 23 da hukumar kula da lafiya a matakin farko waɗanda za su karɓi Naira ₦20,000 a matsayin goron sallah.
A sanarwar wadda Kakakin Gwamnan, Abubakar Bawa ya sanya wa hannu ya bayyana cewar za a fara biyan kuɗaɗen ne daga gobe Alhamis 13 ga wata.
A farkon wannan makon ne dai Gwamnan ya biya ma’aikata albashin watan Yuni da ake ciki domin ba su damar gudanar da Sallah a cikin sauki.