Gwamna Ahmad Aliyu na Jihar Sakkwato ya amince da nadin Sakataren Gwamnati, Shugaban Ma’aikata da wasu mutane biyar a jihar.
Alhaji Bello Sifawa shine sabon Sakataren Gwamnati a yayin da Alhaji Aminu Dikko ya kasance shugaban ma’aikata na Fadar Gwamnati.
Kakakin Gwamnan, Malam Abubakar Bawa ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya baiwa manema labarai a yau Laraba tare da cewar Barista Gandhi Umar, zai yi aiki a matsayin Babban Mataimaki na Musamman kan Sha’anin Mulki da Husaini Gorau a matsayin Mataimakin Gwamna na Musamman (PA).