Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Litinin.
Wannan shi ne karon farko da ya kai ziyara tun bayan ficewarsa PDP zuwa APC.
- An Kaddamar Da Taron Fahimtar Kasar Sin Na Kasa Da Kasa Na Shekarar 2025
- Gwamna Adeleke Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Kefas ya isa Fadar Villa da misalin ƙarfe 2 na rana tare da Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, inda suka yi ganawar sirri da Shugaban Ƙasa.
Ziyarar na zuwa ne kimanin makonni biyu bayan ya fice daga PDP, matakin da ya girgiza siyasar Taraba kuma ya ƙarfafa APC a yankin Arewa maso Gabas gabanin zaɓen 2027.
Tun da farko an shirya taron tarbarsa zuwa APC a ranar 19 ga wata Nuwamba, amma ya ɗage shi, inda ya ce hakan bai dace ba a lokacin da ƙasa ke cikin jimamin sace ɗaliban mata a Maga, a Jihar Kebbi.













