Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 ga majalisar dokokin jihar na kudi N432,523,730.
Da yake gabatar da kasafin kudin mai taken, “kasafin ceto” ga ga alumma a yau Alhamis.
- Sin Za Ta Daidaita Haraji Kan Hajojin Da Ake Shige Da Ficen Su A 2024
- Madaidaitan Ra’ayoyin Xi Jinping Kan Ayyukan Raya Aikin Gona Da Samar Da Abinci
Gwamna Lawal ya ce, N113,134,734 na kashe kudade akai-akai ne wanda ke wakiltar kashi 30 cikin dari.
Da yake karkasa kasafin kudin, Gwamna Dauda ya bayyana cewa ilimi, tsaro, lafiya, da ababen more rayuwa ne ya fi kaso mafi tsoka da nufin ceto jihar daga baragurbin ababen more rayuwa.
Ya yi bayanin cewa kasafin kudin zai ba da fifiko musamman kan ilimi da inganta makarantu l, ya kara da cewa, an kuma kaddamar da Asusun Tsaro tare da daukar masu gadin al’umma 4,300 don tallafa wa jami’an tsaro.
A cewar gwamnan, za a kammala dukkan ayyukan da ake gudanarwa a shekarar 2024 yayin da kuma za a fara sabbin ayyukan tituna a Mallamawa zuwa Bukuyum, Bukuyum zuwa Zoma zuwa Gumi, Maradun zuwa Makera, Kwatarkwashi zuwa Mada da sauransu.
Shima da yake jawabi yayin gabatar da jawabai, kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Nasiru Ismaila Moriki ya bayyana wasu nasarorin da gwamnati mai ci ta samu, ya kuma yabawa gwamna Dauda Lawal bisa hangen nesan ceton alumma da manufofinsa na ci gaban jihar cikin ajandarsa guda shida.
Shugaban majalisar ya kuma amince da kyakkyawar alakar aiki tsakanin bangaren zartarwa da na majalisar dokoki a jihar, sannan ya bada tabbacin za a gaggauta aiwatar da kasafin kudin wanda yanzu ya wuce karatu na biyu.