• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Zamfara Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Garin Mada

Ya sha alwashin hukunta waɗanda suka kashe Malamin 

by Leadership Hausa
2 years ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya ziyarci garin Mada domin yin ta’aziyyar rasuwar babban Limamin garin, Marigayi Sheikh Abubakar Mada.

Idan za a iya tunawa, wasu da ake zargin ’yan banga ne suka kashe Sheikh Abubakar Hassan Mada a makon jiya a garin Mada da ke Ƙaramar Hukumar Gusau ta Jihar Zamfara.

  • Xi Ya Halarci Zama Na Biyu Na Taron Shekara Shekara Na Majalisar NPC
  • Yadda Rayuwata Ta Sauya Bayan Mayar Da Tsintuwar Naira Miliyan 15 – Auwalu

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa Gwamna Lawal ya yi sallar Juma’a ne a masallacin garin Mada.

A cewar sanarwar, Gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayi Sheikh Abubakar Hassan Mada, Hakimin gundumar, da sauran al’ummar yankin.

A yayin jawabinsa ga jama’a bayan sallar Juma’a, Gwamna Lawal ya yi alƙawarin yin duk mai yiwuwa don ganin an yi adalci a kan lamarin.

LABARAI MASU NASABA

Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 

NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan

“Na zo nan ne domin in tabbatar wa mutanen garin Mada cewa gwamnatina ta himmatu wajen ganin an tabbatar da adalci, tare da hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika.

“Babu wani abu da za a bari wajen ganin an tabbatar da adalci a kan kisan Sheikh Abubakar. Za mu yi aiki tuƙuru don ganin cewa marigayi Sheikh da iyalansa sun samu adalcin da ya kamata,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta nakalto gwamnan yana cewa, “Bana Gusau lokacin da lamarin ya faru, amma bayan na samu wannan labari mai tada hankali, nan take na tuntuɓi shugabannin hukumomin tsaro da abin ya shafa a jihar domin ɗaukar matakin da ya dace”.

“’Yansanda sun fara gudanar da bincike cikin gaggawa kan kisan gillar. Na rantse da Allah za mu tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi a wannan ɗanyen aikin, za a hukunta shi,” in ji sanarwar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

2023: Gwarazan Jam’iyyu A Karon Battar Zaben Shugaban Kasa
Manyan Labarai

Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 

November 3, 2025
Likitoci
Labarai

NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan

November 3, 2025
Kano
Manyan Labarai

Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

November 3, 2025
Next Post
Kungiyar Lauyoyi Ta Tabbatar Da Fara Gurfanar Da Masu Laifukan Zaben 2023

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.