• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Zamfara Ya Yi Kira A Kara Yawan Sojoji A Jihar Don Yaki Da ‘Yan Bindiga

bySadiq
2 years ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi kira da aka yawan sojojin da aike jihar, domin magance ayyukan ‘yan bindiga.

Gwamnan ya ziyarci Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Christopher Gwabin Musa, a Hedikwatar tsaro da ke Abuja.

  • Mutane 11 Sun Rasu, 30 Sun Jikkata A Rikicin Kabilanci A Filato – Gwamnati
  • HOTUNA: Yadda Jami’an Tsaro Suka Lalata Haramtacciyar Matatar Danyen Mai A Ribas

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa Gwamnan ya gana da Babban Hafsan tsaron ne domin tattauna batun matsalar tsaro a Jihar Zamfara.

A yayin taron, Gwamna Lawal ya bayyana damuwarsa kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare a wasu sassan Jihar Zamfara.

Ya kuma yi kira ga Babban Hafsan tsaron ƙasar da ya tura ƙarin sojoji da makaman da suka dace zuwa jihar.

LABARAI MASU NASABA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

“A yau na zo nan ne domin tattaunawa kan matsalar rashin tsaro da ta addabi Jihar Zamfara. Na zo nan a ‘yan watannin da suka gabata saboda wannan batun.

“A ’yan kwanakin nan an sha fama da matsalar hare-haren ’yan bindiga a wasu yankunan jihar.

“A cikin makon nan an kai wani hari a Ƙaramar Hukumar Tsafe, wanda ya yi sanadin asarar rayuka, ciki har da Jami’in Rundunar Kare Jama’a “Askarawan Zamfara” (CPG), sannan wasu ’yan bindiga sun ƙone motocin sojoji da suka haɗa da na jami’an CPG.

“Muna fama da ƙarancin sojoji a Zamfara saboda an sake tura wasu jami’an yankin Arewa maso Gabas.

“Manoma ba sa iya noma gonakinsu, kuma hare-haren da ake ci gaba da kaiwa ya janyo asarar rayuka da dama.

“Ina so in yi amfani da wannan dama wajen kira gare ku da ku haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tura ƙarin sojoji zuwa Zamfara, irin wannan mataki na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro da kuma dawo da zaman lafiya a jihar.

“Tsarin jami’an tsaro babu shakka zai kwantar wa jama’a hankali tare da karya gwiwar masu aikata laifuka daga aikata munanan ayyukansu.

Da yake mayar da martani, Babban Hafsan tsaron ƙasa, Janar Christopher Gwabin Musa, ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Lawal na yaƙi da ’yan bindiga a Zamfara.

Ya ce: “Ina godiya ga ƙoƙarin da ka ke yi na yaƙar rashin tsaro. Muna shirin daidaita al’amura a Zamfara kamar yadda muka yi a Maiduguri.

“Muna tattaunawa da dukkanin Kwamandoji da masu ruwa da tsaki don magance matsalar hare-haren, wanda ke matuƙar sanya ɓacin rai,” in ji Janar Musa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Next Post
Muna Sane Nijeriya Ta Tsare Ɗan Kasarmu Ma’aikacin Binance – Amurka

Muna Sane Nijeriya Ta Tsare Ɗan Kasarmu Ma'aikacin Binance - Amurka

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version