Tsohon gwamnan Jihar Sakkwato kuma Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, ya zargi gwamnatin tarayya da amfani da EFCC domin tsoratar da shi ya amince ya koma jam’iyyar APC. Ya ce wannan yunƙuri ba zai hana shi da magoya bayansa ci gaba da amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba su wajen kare dimokuraɗiyya da ceto Nijeriya ba.
Tambuwal, wanda ya jagoranci yaƙin neman zaben shugaban ƙasa na Atiku Abubakar a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a 2023, ya bayyana hakan ne yayin taron tarɓarsa da magoya baya suka shirya a gidansa, ranar Alhamis a Sakkwato.
Ya ce zargin satar Naira biliyan 189 ba shi da tushe, yana mai bayyana cewa duk kuɗin da suka samu a lokacin gwamnatinsa an yi amfani da su wajen ayyukan ci gaban al’umma, kuma mutanen Sakkwato sun sani.
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci Sun Kashe Wani Mutum Da Jikkata Wasu Da Dama A Sokoto
- Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi
Ya ƙara da cewa, “Idan ba don na tsaya tsayin daka wajen hidimar jama’a ba, da ba a riƙa bibiyata da irin wannan bita da ƙulli ba. Jam’iyyar haɗaka da muka gina za ta yi nasarar kawar da gwamnatin Tinubu a 2027, domin burinmu shi ne jama’a su haɗa kai wajen ceto ƙasar nan.”
Tsohon kakakin majalisar wakilai ta bakwai ya jaddada cewa a tsawon shekaru 22 da ya shafe yana riƙe da muƙamai a siyasa, ba a taɓa zarginsa da wata badaƙala ba, yana mai cewa su ne suka kawo tsarin da ya tabbatar da tsaron jama’a lokacin da suka karɓi mulki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp