Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa Juma’a, 18 ga watan Afrilu, da Litinin 21 ga watan Afrilu, 2025, za su kasance ranakun hutun bikin Esta.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya.
- Za A Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Malay
- An Yanke Masa Hukuncin Ɗaurin shekaru 2 A Gidan Yari Saboda Yunƙurin Daɓa Wa Mahaifinsa Almakashi A Kano
Ya taya dukkanin Kiristoci murnar bikin Esta tare da fatan alheri a lokacin bukukuwan.
Ministan ya buƙaci ’yan Nijeriya da su yi amfani da hutun wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
Ya kuma ƙarfafa gwiwar jama’a su wanzar da soyayya da tausayi ga maƙwabtansu.
Ya tabbatarwa da ’yan Nijeriya cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nan daram bisa ƙudirinsa na “Renewed Hope Agenda” domin inganta rayuwar ’yan ƙasa da bunƙasa ƙasa baki ɗaya.
Ministan ya ƙara da cewa bukukuwan Esta na ba da damar yin nazari da kuma ƙarfafa zumunci a tsakanin dangi da al’umma.
Gwamnati ta buƙaci jama’a da su gudanar da bukukuwan cikin lumana da kwanciyar hankali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp