Gwamnatin tarayya ta umurci mataimakan shugabannin jami’o’in da su sake bude makarantunsu domin dalibai su koma karatu.
Sanarwar ta fito ne a wata takarda mai dauke da sa hannun Daraktan kudi da asusu na hukumar jami’ar ta kasa (NUC), Sam Onazi, a madadin babban sakataren hukumar Farfesa Abubakar Rasheed.
- Zamu Rufe Filayen Jiragen Sama Har Sai An Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU – NANS
- Kotu Ta Dage Karar Da Gwamnatin Tarayya Ta Kai ASUU
Wasikar zuwa ga dukkan mataimakan shugabannin da shugabannin majalissar gudanarwar jami’o’in tarayya, LEADERSHIP ta ci karo da takardar a safiyar yau Litinin.
Ya kara da cewa: “Tabbatar da cewa ‘yan kungiyar ASUU da su koma/fara karatu da dawo da ayyukan yau da kullun na cibiyoyin Jami’o’i daban-daban. ”
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne kotun da’ar ma’aikata a Nijeriya ta umurci kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ta janye yajin aikin da take yi a fadin kasar tare da komawa aji.
Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki domin matsa lamba kan bukatar inganta kudaden da ake baiwa jami’o’in, da batun albashin malaman jami’o’i da dai sauransu.
An dai kawo karshen tarukan da aka yi tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya cikin rashin jituwa.
Sakamakon haka gwamnatin tarayya ta garzaya kotu domin kalubalantar yajin aikin.
Gwamnati ta bakin lauyanta, James Igwe, ya roki kotun da ta dakatar da ASUU daga daukar wasu matakai dangane da yajin aikin, har sai an yanke hukunci kan karar.