Bayan shafe wata bakwai kungiyar malaman jami’a ta ASUU na yajin aiki, yanzu haka kungiyar dalibai ta Nijeriya NANS ta bayyana cewa za ta rufe dukkan filayen jiragen saman kasar nan domin hana tashi da saukar jiragen, har sai an warware tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a taron da ta yi a Akure karshen wannan makon. Shugaban kungiyar daliban masu fafutukar kawo karshen yajin aikin, Ojo Raymond Olumide, ya bayyana haka loacin da yake gana wa da manema labarai.
Shugaban ya ce, za su ci gaba da zanga-zangar, har sai hakarsu ta cimma -ruwa.
Talla