Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta bai wa gwamnonin jihohin ƙasar nan 36 fiye da naira biliyan 570 domin bunkasa shirye-shiryen rage radadin matsin rayuwa a fadin Nijeriya.
Tinubu ya fayyace hakan ne a yau Lahadi yayin jawabinsa da ya yi wa ‘yan kasa kan zanga-zangar da ake ci gaba da gudanar wa a fadin kasar.
- Tsadar Rayuwa: Atiku Ya Yi Allah Wadai Da Harbin Masu Zanga-zanga
- Tinubu Zai Yi Wa ‘Yan Nijeriya Jawabi A Ranar Lahadi
Zanga-zangar dai, an shirya fara ta ne a tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024 domin nuna kin amincewa da kuncin rayuwa da ake fama da shi a fadin kasar.
Daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta bullo da su don habbaka tattalin arziki da more rayuwa, Tinubu ya ce, “kimanin masu ƙananan sana’o’i 600,000 ne suka samu tallafin bashi daga gwamnatin tarayya.”
Ya ƙara da cewa “yanzu haka gwamnati na tantance masu matsakaitan sana’o’i mutum 75,000 domin samun bashin naira miliyan 1 ga kowanennsu, da za su fara samu cikin wannan wata na Agusta.
”Bugu da kari, masu manyan kamfanoni za a ba su bashin naira biliyan 1 kowannesu don bunƙasa kasuwancinsu”.