Hukumar kula da dakon man Fetur (NMDPRA) ta sanar da cewa daga ranar 1 ga Maris, 2025, za a haba manyan motocin tankokin mai masu lita 60,000 a kan titunan Najeriya ba. Wannan mataki yana da nufin rage yawaitar hadurran manyan motocin mai, waɗanda ke haddasa gobara da asarar rayuka. Haka kuma, daga karshen shekarar 2025, an haramta lodin fiye da lita 45,000 na mai a kowaccee matatar lodin kayayyaki.
Shugaban rarraba kayayyakin man fetur a NMDPRA, Ogbugo Ukoha, ya bayyana cewa matakin ya zama dole sakamakon yawaitar haɗurran manyan motocin dakon mai a ƙasar. Ya ce an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro, hukumar FRSC, da ƙungiyoyin NARTO da , da sauran masu ruwa da tsaki a harkar safarar mai.
- Abin Da Ya Sa Masu Ruwa Da Tsaki Suka Gana Da Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur
- Matatar Man Ɗangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦890
Sai dai ƙungiyar masu motocin dakon mai (NARTO) ta nuna damuwarta, tana mai cewa wannan matakin zai jawo asarar sama da Naira biliyan 300 ga masu motocin safarar mai. Shugaban NARTO, Yusuf Othman, ya ce ba girman motocin bane ke haddasa haɗurra ba, illa kuwa halin da tituna, da motocin da direbobi ke ciki.
Rahotanni sun nuna cewa tun daga shekarar 2009, an samu haɗurran motocin dakon mai guda 172, inda mutane 1,896 suka rasa rayukansu. Kawo yanzu, shekarar 2024 ita ce mafi muni, inda a ƙalla mutane 266 suka mutu sakamakon fashewar tankokin mai, ciki har da gobarar da ta hallaka mutum 181 a Jigawa a watan Oktoba.
Duk da ƙorafin masu motocin, gwamnati ta dage cewa dole ne a ɗauki matakan rage yawan haɗurran, inda take duba wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen sauya motocin da ake son hana amfani da su.