Majalisar Kasa, ta kara yawan adadin kudaden shiga da take bukata Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) za ta tara a 2025, zuwa Naira tirilyan 25.
Ta dauki wannan matakin ne, bayan da Shuagaban Hukumar Zacch Adedeji, ya shedawa kwamtin kudi na hadaka na Majalisar cewa, Hukumar kudaden shigar da Hukumar ta tara a 2024, sun wuce yawan Naira tiriliyan 19.4, duba da yadda dokar kudi ta kasar ta 2024, ta tanada.
- Shirin Tallafinmu Ga Nijeriya A 2025 Zai Kai Ga Asalin Mabukata – Wakilin MDD
- Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Arewa Maso Gabashin Kasar Sin Gabanin Bikin Bazara
Adedeji, wanda ya shedawa kwamitin hakan ne, a ranar Laraba yayin da yake yiwa kwamtin bayani kan kokarin da Hukumar ta yi, na tara harajin.
Hakan ne ya sanya, kwamitin ya umarci Hukumar ta tara harajin da ya kai Naira tiriliyan 25 a 2025.
Mataimakin Shugaban kwamtin kudi na majalisar wakilai Hon. Saidu Musa Abdullahi, ya yaba da kokarin Hukumar wajen tara harajin, tare da kuma shawartar Hukumar da ta yi nazari a kan irin tsarin zamani na tara haraji na kasar Afirka ta Kudu, wanda ya ce, tsarin na Afrika ta Kudu, na bai wa kasar, damar tara haraji sama da yadda akan sa ran tarawa kasar.
“Zamu baku dukkanin goyon bayan da ya kamata kan sauye-sauyen ku na biyan haraji, amma dole ku ksance kara kaimi, wajen Tarawa kasar haraji. “Inji Musa.
Shi kuwa dan majalisa Hon. Benedict Sapele, ya dan nuna rashin gamsuwarsa kan cewa, idan har Hukumar ta kara mayar da hankali wajen tara haraji, ba sai Gwamnatin Tarayya ta ciwo bashi wajen cike gibin da ake dashi, a cikin kasafin kudi ba.
A martaninsa, Adedeji ya bayyana cewa, yawan karbar haraji da sauran Hukumomin Gwamnati ke yi ne, ke haifar da zurarewar kudade, sai dai ya yi nuni da cewa, za a iya rage hakan ne, idan sabon kudurin haraji, ya zamo doka.