Gwamnatin Jihar Adamawa, ta dakatar da lasisin wasu cibiyoyin koyar da aikin kiwon lafiya takwas, da ta ce sun gaza cika ka’idojin koyar da aikin jinya a jihar.
Cibiyoyin da lamarin ya shafa sun hada da Kwalejin koyon aikin jinya ta Fat-Hur-Rahman of Health Sciences and Technology, College of Health Technology, Almashkur International Academy, da School of Health Technology Kazaure.
- Kumbon Tianzhou-7 Ya Hade Da Tashar Sararin Samaniyar Sin
- Tinubu Ya Gana Da Ganduje Da Shugabannin APC Na Kano A Villa
Akwai kuma Savannah Model Collage of Health Sciences and Technology, Freetown Avenue, Jimeta Central College of Health Science and Technology, School of Health Technology, Nafan College of Health Science and Technology, da Bell Dome College of Health Sciences and Technology.
Da yake bayyana dalilin soke lasisin, babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar Barista Isuwa Misali, ya ce an dauki matakin ne domin dakile yaduwar cututtuka da kuma tsaftace cibiyoyin kiwon lafiya a jihar bisa manufar gwamna Ahmadu Fintiri na inganta harkar kiwon lafiya.
Ya ci gaba da cewa “duk kwalejojin kiwon lafiyar da aka rufe ba su cika sharudan da ake bukata na kafa cibiyoyin horas akin kiwon lafiya ba.
“Cibiyoyin kiwon lafiya dole su samar da kwararru, masana fannin kiwon lafiya 10, cibiyar shakatawa, filin motsa jiki, masaukai da sauran abubuwan bukata.
“Kwalejojin da abin ya shafa za su iya hada kai da ma’aikatar lafiya, don cika dukkan ka’idodin da suka kamata, don kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta kiwon Lafiya, da samun izinin gudanar da aiki” in ji Misali.