Hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta kasar Sin (CMSA) ta bayyana cewa, kumbon Tianzhou-7 na kasar Sin, ya kammala daidaitawa, tare da hadewa da tashar binciken sararin samaniya ta Tiangong yau Alhamis.
A cewar hukumar CMSA, kumbon Tianzhou-7 ya yi nasarar hadewa da muhimman sashen Tianhe ne da karfe 1 da mituna 46 na safe, agogon birnin Beijing.
- Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Mai Dorewa Da Inganci Na Kara Ba Da Gudummawa Ga Ci Gaban Duniya
- Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Haramta Wa Sarakuna Bada Izinin Hakar Ma’adanai
Bayanai na cewa, ma’aikatan kumbon Shenzhou-17 dake cikin tashar sararin samaniya, za su shiga cikin kumbon, tare da jigilar kayan dake cikinsa kamar yadda aka tsara. (Mai fassara: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp