Da akwai yiyuwar shirin gwamnatin tarayya na sayar da danyen mai a kan naira zai ci gaba, inda majiyoyi suka tsegunta wannan batun a ranar Litinin tare da cewa dukkanin bangarorin da abun ya shafa za su koma teburin tattaunawa kwanan nan domin ganin sake dawo da harkar danyen mai a kan farashin Naira.
Hada-hadar cinikayyar danyen mai a kan naira na wata shida tsakanin gwamnatin tarayya, kamfanin kula da albarkatun mai da matatar man dangote ya kawo karshen ne dai a ranar 31 ga watan Maris din 2023.
- Sarki Sanusi Ya Yabawa Gwamna Yusuf Kan Manufofin Haɓaka Jama’ar Kano
- Nijar Ta Fice Daga Rundunar Tsaro Ta Haɗin Kai MNJTF
Tuni dai matatar man dangote ta dakatar da sayar da man fetur a kan naira sai dala, sakamakon cewa ita da dala take sayen danyen man.
Wannan na zuwa ne a yayin da wani rahoto da S&P Global ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa matatar dangote na sarrafa kusan ganga 400,000 a kowace rana ta danyen mai a shekarar 2025, inda kusan kashi 35 cikin 100 na wannan danyen mai din kamfanin na sayowa ne daga kasashen waje.
Hakan na nufin kamfanin na shigo da gangar danyen mai kusan ganga 140,000 a kowace rana da jimillar ganga miliyan 12.6 a cikin watanni uku.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya.
“Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci gaba saboda na gano cewa tsarin ya yi tasiri sosai ba kawai a kan farashin mai ba, har ma da kyautata ci gaban tattalin arziki.
“Bugu da kari, kwamitin yana jiran hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya ta gabatar da rahoton aikin da aka ba ta dangane da wannan manufar. Da zarar an yi haka, abu na gaba shi ne a duba abun da za a yi na gaba kan wannan batun hada-hadar mai da kudin naira,” cewar majiyar wanda ya nemi a dakaye sunansa.
Idan za a tuna dai, a ranar 1 ga watan Oktoban 2024 ne gwamnati ta fara sayar da danyen mai a kan naira ga matatar man dangote domin inganta samar da man fetur, lamarin ya kai ga taimaka wa kasar nan da samun rarar miliyoyi na dala da take narkawa wajen sayo danyen mai daga kasashen waje, kuma shirin ya taimaka sosai wajen samun ragi kan farashin fetur.
A baya-bayan nan, kakakin kamfanin NNPC, Olufemi Shoneye yayin da ke fashin karin haske kan batun karewar hada-hadar cinikin, inda ya ce, “Bari na fayyace wannan lamarin, daman an kulla yarjejeniya ce na watanni shida, ya danganci wadatar danyen mai, kuma zai kare ne a karshen watan Maris na 2025.
“Tattaunawa na ci gaba da gudanar kan yadda za a kulla sabuwar yarjejeniya.
“A karkashin wannan yarjejeniyar, NNPC ya samar da danyen mai sama da ganga miliyan 48 ga matatar dangote tun watan Oktoban 2024.
“A takaice, NNPC ya samar da danyen mai ganga miliyan 84 ga matatar tun lokacin da ta fara aiki a shekarar 2023.
“NNPC ya himma wajen samar da danyen mai ga matatun mai na cikin gida a bisa tsarin yarjejeniya da sharuddan da aka cimma,” ya shaida.
Kazalika, rahoton S&P ya nuna cewa matatar mai ta dangote ta sayo danyen mai na farko ne daga kasar Burazil da Ekuatorial Guinea.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp