Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyar samar da ‘Renewed Hope Cultural Villages’ a dukkan jihohin kasar nan 36 domin bunkasa al’adun gargajiya na Nijeriya.
‘Renewed Hope Cultural Villages’ shiri ne da zai farfado da muhimman wuraren tarihi na al’ada a duk fadin Jihohi 36 na tarayyar Nijeriya
- Tsawa Ta Kashe Makiyayi Da Shanu A Kudancin Kaduna
- Yawan Kayayyakin Da Aka Yi Hada-hadarsu A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Sin A 2024 Ya Ci Gaba Da Kasancewa Na Farko A Duniya
Mataimaki na musamman ga ministan fasaha, al’adu, yawon bude ido, da tattalin arziki a bangaren nishadantarwa, Abiola Jagunlabi, a wata hira da manema labarai a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ya bayyana cewa, shirin wani bangare da zai mayar da hankali kan kiyaye al’adun gargajiya, karfafa yawon shakatawa, da kuma bunkasa tattalin arziki.
Jagunlabi ya ce za a gudanar da shirin ne tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi domin mayar da wuraren tarihi zuwa wuraren shakatawa domin samar da kudin shiga wanda hakan zai haifar bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi a fannin fasaha da nishadi.
Ya bayyana cewa, aikin zai mayar da hankali ne wajen maidowa tare da kiyaye wuraren tarihi, kayayakin tarihi, da inganta ilimin al’adu da inganta sana’o’in cikin gida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp