Ma’aikatar aikin noma da raya karkara ta shelanta cewa, tana son a noma shinkafa ‘yar gida tan miliyan 34 a kakar noman shekarar 2023.
Wannan adadin da ma’aikatar ta sanar ba kunshe ne a cikin sabon tsarin bunkasa noman shinkafa na kasa daga shekarar 2022 zuwa shekarar 2023 (NRDS) wanda ma’aikatar ta kaddamar a kwanan baya.
- Gwamna Gombe Ya Taya Kiristoci Murnar Kirsimeti, Ya Hore Su Kan Zaman Lafiya
- Illolin Rashin Hadin Kan Magidanta (2)
Tsarin dai na son ya cim ma burin kara habaka noman na shinkafar da sarrafa ta a kasar nan ta hanyar yin amfani da kayan aikin noma na zamani.
Bugu da kari, kamar yadda aka tsara nama da shekarar 2023, ana kuma sa ran a yi renonon irin shinkafar tan 66.6 ko kuma tan 5,327.3, inda kuma za a samar da ingancin Irin shinkafar kashi 80 a cikin dari.
Tsarin wanda aka kaddamar da shi a birnin tarayyar Abuja, a jawabinsa a wajen kaddamarwar, karamin minista a ma’aikatar aikin noma da raya karkara Mustapha Baba Shehuri ya bayyana cewa, tsarin na (NRDS) zai taimaka wajen a samar da alkibla domin a kara bunkasa noman shinkafar a kasar nan tare da wadata kasar nan da shinkafar. Mustapha ya ci gaba da cewa, har ila yau, tsarin zai taimaka wajen kara samar da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya da kara noman shinkafar da za fitar zuwa kasashen duniya domin a sayar da ita.
A cewar Mustapha, Nijeriya ta jima da shiga cikin shirin noman shinkafa na nahiyar Afirka wato (CARP), inda ya sanar da cewa, wannan shirin, ya mayar da hankali ne wajen ganin ana noma shinkafa ‘yar gida a bisa ka’ida da kuma ci gaba da wanzar da aikin noman shinkafa tare da yin gasar nomanta a tsakanin kasashen da ke a nahiyar Afirka.
“Tsarin na (NRDS) zai taimaka wajen a samar da alkibla domin a kara bunkasa noman shinkafar a kasar nan tare da wadata kasar nan da shinkafar”.
Karamin ministan ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki da ke a cikin shirin na (CARP), da su tabbatar da sun gudanar da shirin a aikace, musamman domin amfanuwar kasashensu.
Ya yi nuni da cewa, wannan hadakar a tsakanin kasashen na Afrika don a bunkasa noman shinkafar, zai taimaka matuka wajen kara habaka noman shinkafa a daukacin kasashen ciki har da Nijeriya.
“Nijeriya ta jima da shiga cikin shirin noman shinkafa na nahiyar Afirka wato (CARP), inda ya sanar da cewa, wannan shirin, ya mayar da hankali ne wajen ganin ana noma shinkafa ‘yar gida a bisa ka’ida da kuma ci gaba da wanzar da aikin noman shinkafa tare da yin gasar nomanta a tsakanin kasashen da ke a nahiyar Afirka”.
“Wannan hadakar a tsakanin kasashen na Afrika don a bunkasa noman shinkafar, zai taimaka matuka wajen kara habaka noman shinkafa a daukacin kasashen ciki har da Nijeriya”.