Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya jagoranci rantsar da kantomomin raya ci gaban karkara na kananan hukumomi 21 guda 50, ranar Litinin.
Rantsuwar kama aikin wanda kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin jihar, Barista Afraimu Jingi, ya aiwatar a gidan gwamnatin, ya gargadi kantamomin da su mutunta alkawarin gudanar da aiki da gaskiyar da suka yi.
- Kyautar CAF ta 2023: Super Falcons Ta Lashe Kyautar Tawagar Mata Mafi Kwazo A Afirka.
- Kuri’ar Kin Amincewar Amurka Ta Tsagaita Wuta A Gaza Adawa Ce Ga Bukatar Bil’adama
Gwamnan wanda mataimakiyarsa Farfesa Kaletapwa Farauta ta wakilta, ta kuma gargadi kantamomin raya karkarar, da su yi aiki bisa tsare-tsare da masu ruwa da tsakin yankunan da suka fito, da cewa hakan zai sa jama’a su amfana da gwamnatin.
Haka kuma gwamnan ya gargadi kwantomomin da cewa “aikata wani abu sabanin wanda kuka dauki rantsuwa a kai, ba zai ba ku damar yin abin da ya kamata ba,” inji gwamnan.
Da yake jawabin godiya a madadin sabbin kwantomomin raya ci gaban karkarar, Mista Emmanuel Dauda, ya gode wa bangaren zartaswar gwamnati da ‘yan majalisun jihar bisa zabo su da nada su mukaman da aka yi.