Jam’iyyar PDP ta caccaki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda rashin dubarun shugabanci, inda ta ce gwamnatin APC ta kara ingiza ‘yan Nijeriya da dama cikin bakin talauci.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba shi ya bay-yana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja. Ya ce dabi’u da manufofin jam’iyyar APC na yaudara tun bayan ka-fuwarta a shekarar 2014 da kuma hawan mulkita a 2015, ba wai kawai ta sanya Nijeriya ta zama cibiyar talauci a duniya ba, har ma ta jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin hali ta hanyar manufofinta mara su kyau.
- Sin Ta Mikawa Gwamnatin Sudan Kashin Farko Na Tallafin Jin Kai
- Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ya Amsa Tambaya Game Da Taron Ministocin Muhalli Da Yanayi Na G20
A cewar Ologunagba, jawabin shugaban kasa na ranar Litini, kokari ne kawai na kawar da hankalin ’yan Nijeriya daga halin kuncin da suke ciki da kuma yawan alkawuran da gwamnatin Tinubu ta yi.
Ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta jajirce ne kawai ga muradun kasashen waje wanda suke bisa turbar kuskure da ba za su haifar wa kasar nan da mai ido ba.
Ya kara da cewa jawabin shugaban ba shi da wani tanadi na tsaron yankunan bakin teku da kuma jigilar ruwa a yankunan kogin, wanda ya kasance tubulin tat-talin arzikin Nijeriya.
Ya ce APC ta hau mulki ne ta hanyar farfaganda kuma ba ta cika alkawuran da ta yi wa ‘yan Nijeriya ba har yau.
“A yammacin Litinin, Sanata Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC ya kashe wa ‘yan Nijeriya fatan da suke da shi, musamman magoya bayansa da ke cikin rudani a yanzu, tare da gabatar da jawabinsa na kare kai daga munanan tsare-tsare da kuma manufofinsa mara amfani ga kasar nan. Jam’iyyar PDP koka kan yadda za a samu irin wannan rashin adalci wanda ya kara nuna rashin dabarar shugabanci da mayar da hannun agogo baya a kasar nan.
“Jam’iyyar PDP ta yi matukar kaduwa da wannan jawabi na shugaban kasa na alkawuran karya da ya yi.
“Yan Nijeriya sun san cewa jam’iyyar APC tare da Tinubu ba za su iya cika wadan-nan alkawuran da suka dauka ba, sun mayar da al’ummarmu wata cibiyar talauci ta duniya, inda sama da ‘yan kasa miliyan 100 ba za su iya cin abincin yau da kul-lum ba sakamakon hauhawar farashin kayayyakin masarufi. Tabbas babu wani abu sabo daga cikin kalamun Shugaba Tinubu, alkawaruka ne kawai a takarda amma ba za a iya zantar da su ba.
“Jawabin da Shugaban kasa ya yi babu wasu hanyoyi na kawo mafita sai dai ‘yan Nijeriya ci gaba da shan wahala da tsadar rayuwa sakamakon rashin sanin maka-man aikin gwamnatin APC.