Gwamnatin Jihar Bauchi ta amince da matsayar da Masarautar Bauchi ta ɗauka na ɗage bikin Hawan Daushe na bana, wanda ake yi a lokacin bikin salla ƙarama.
Sanarwar da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Juma’a ta bayyana cewa masarautar ce, ta yanke wannan shawara ba tare da tuntuɓar gwamnati ba tun da farko.
- Gaggan Masu Garkuwa Da Mutane 10 Da Kayan Aikinsu Sun Shiga Hannu A Kano
- Gobara Ta Kashe Yaro A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Maiduguri
Hawan Daushe ya kasance wata al’ada da ake yi duk bayan Sallah, inda sarakuna da masu riƙe da sarautu ke hawan dawakai cikin shigar alfarma, tare da nuna al’adun gargajiya.
Wannan biki na jan hankalin jama’a da masu yawon buɗe ido.
Gwamnatin ta bayyana cewa tun da farko ta shirya tsaf domin tabbatar da tsaro a yayin bukukuwan Sallah.
Sai dai, bisa ladabi da girmamawa ga masarautu, Gwamna Bala Muhammad ya amince da roƙon ɗage Hawan Daushe.
Duk da haka, gwamnatin ta nuna damuwarta kan yadda ba a tuntuɓe ta ba kafin yanke wannan shawara.
Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da aiki tare da sarakuna domin kyautata zamantakewa da ci gaban jihar.
Ga mutanen da wannan ɗagewa ta shafa, gwamnati ta fahimci damuwarsu, amma ta yi alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace a nan gaba don kauce wa irin wannan matsala.
Gwamnan ya yi fatan jama’a za su yi bikin Sallah cikin lumana da farin ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp