Majalisar zartarwar jihar Bauchi (SEC) ta amince da fara biyan naira dubu 32 a matsayin mafi ƙarancin kuɗin fansho na wata-wata ga tsofaffin ma’aikatan gwamnatin jihar.
Shugaban ma’aikatan jihar Bauchi (HoS), Barista Mohammed Sani Umar, shi ne ya sanar da amincewar yayin da ke shaida wa ‘yan jarida sakamakon zaman majalisar wanda ya gudana a jiya, ya bayyana cewar ƙarin ya biyo bayan amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi da gwamantin tarayya ta yi ne a baya.
- Ƴansandan Libya Sun Kama Ƴan Nijeriya Biyu Kan Zargin Fashi
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Kawo Wa Afirka Fatan Warware Matsalar Karancin Wutar Lantarki
“Majalisar zartarwa ta jihar Bauchi ta amince da fara aiwatar da sabon ƙarin mafi ƙarancin kuɗin da fansho daga Naira N12, 000 zuwa N32, 000, ƙarin wanda ya ma ya zarce N19, 000 ga tsofaffin ma’aikatanmu.
“A yau (Ranar Laraba) majalisar zartaswa ta yi la’akari da batun ƙarin kuɗin fansho ga tsofaffin ma’aikatan jiharmu da suka yi ritaya, hakan ya biyo bayan ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata da kuma mafi ƙarancin kuɗin fanshi na ƙasa da gwamnatin tarayya ta amince da su,” in ji shugaban ma’aikatan.
Barista Sani ya ƙara da cewa, tun ma kafin wannan ƙarin, hatta adadin mafi ƙarancin fansho da jihar Bauchi ke biya a baya na Naira dubu 12, wasu jihohi da dama ba su ma biyan irin wannan, ga kuma sabon ƙari da suka amince dukkan domin kyautata rayuwar tsofaffin ma’aikata a faɗin jihar.
Ya misalta amincewar a matsayin kyakkyawar yunƙurin gwamna Bala Muhammad na kyautata rayuwa da jin daɗin tsofaffin ma’aikatan jihar, ya ce, karin zai kuma yi daidai da halin da tattalin arziki ya ke ciki a zahirance.
“Tabbas ƙarin mafi ƙarancin kuɗin fansho zuwa Naira dubu talatin da biyu zai kyautata rayuwar tsofaffin ma’aikatanmu da suka bayar da gudunmawarsu sosai wajen ci gaban jihar nan a lokacin da suke bakin aiki.
“Gwamna ya nuna himma sosai wajen kyautata rayuwar ma’aikata da tsofaffin ma’aikata a jihar Bauchi. Yana fifita walwala da jin daɗinsu sosai,” Umar ya tabbatar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp