A ranar Juma’a ne Gwamnan Jihar, Bauchi Bala Muhammad, ya sanya hannu kan wasu dokoki 12 da majalisar dokokin jihar ta zartas, cikin dokokin har da wanda a aka amince da kafa kungiyar ‘yan sintiri da na tallafa wa matasa a fadin jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa, babban makasudin kafa dokar shi ne don tabbatar da tsaro tare da taimaka wa kokarin da jami’an tsaro ke yi na fattakar masu aikata laifuka, kuma za a yi kokarin samar da hanyoyin samar wa da matasa ayyukan yi don su dogara da kansu a harkokin rayuwa na yau da kullum.
- Gwamnatin Bauchi Ta dauki Daliban Likitanci 252 Aiki
- Dalibi Ya Daba Wa Wasu Dalibai 2 Wuka A Kan Musun Kwallon Kafa A Bauchi
Sauran dokokin sun hada da na kafa hukumar fansho ta jihar da kananan hukumomi ta shekarar 2022; da dokar kafa hukumar raya manyan biranen jihar.
Gwamnan ya mika godiyarsa ga majalisar dokokin jihar kan yadda suka yi nazari tare da amincewa da dokokin, ya kuma yi fatan ci gaba da samun hadin kai tsakanin bangaren majalisar da na gwamnati.