Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da ba da hutun kwanaki biyu ga daliban makarantun jeka-ka-dawo da suke karkashinta domin samun sararin gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar Asabar.
Kwamishiniyar ma’aikatar ilimi ta jihar, Dakta Jamila Muhammad Dahiru ce, ta bayyana hakan ga manema labarai a Bauchi.
- Me Ya Sa Samari Ke Wa ‘Yan Matan Yanzu Kallon Zawarawa?
- Buhari Da Tsofaffin Shugabannin Kasa Sun Bukaci ‘Yan Takara Su Karbi Sakamakon Zabe
Ta ce, an ba da hutun ne domin Malamai da iyayen yaran su samu damar yin zabe.
Sannan kuma wasu daliban za su yi tafiya da iyayensu zuwa garuruwa da kauyukansu domin kada kuri’a.
Sannan ta ce a cikin daliban akwai wadanda shekarunsu ya kai na jefa kuri’a don haka wannan hutun zai ba su damar yin zabe.
Kazalika, ta sanar da cewa gwamnatin ta kuma sake ba da hutun kwanaki biyu ga daliban makarantun jeka-ka-dawo a lokacin zaben gwamnan Jihar da na ‘yan majalisun dokoki da zai gudana a ranar 11 ga watan Maris.
“Bisa wannan, daliban makarantun jeka-ka-dawo za su kasance a gida a ranar Juma’a 24 da Litinin 27 ga watan Fabrairu, 2023 a matsayin hutun zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a gudanar a ranar Asabar.
“Ga zaben gwamna da na ‘yan majalisun jiha kuma, dalibai za su kasance a gida a ranar Juma’a 10 da ranar Litinin 13 ga watan Maris 2023, don haka harkokin karatu za su kankama a ranar Talata 14 ga watan Maris.”
Jamila ta ce, daliban makarantun kwana da suke jihar za su kasance a cikin makarantunsu a wannan lokaci.
Kwamishiniyar ta yi amfani da wannan damar wajen nanata aniyar gwamnatin Jihar Bauchi na inganta ilimi, walwala da jin dadin Malamai gami da bayar da ilimi mai nagarta.
Ta yi fatan a yi zabe cikin kwanciyar hankali a dukkanin matakai.