Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi, ya amince da daukar dalibai 252 aikin likitanci a jihar.
Wata sanarwa da jami’in yada labarai na shugaban ma’aikatan Jiha, Umar Sa’idu, ya raba wa manema labarai a Bauchi a jiya, ya ce wannan na daga cikin muradin gwamnatin yanzu na samar da ayyukan yi ga matasa, har ma da inganta kiwon lafiya, tun daga tushe.
- An Sauya Wa Ka’aba Sabuwar Rigar Da Kudinta Ya Kai Dala $6.5m
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutun 6, Sun Bukaci Miliyan 50 Matsayin Kudin Fansa A Katsina
Shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Yahuza Adamu Haruna, ya tabbatar da cewa ofishinsa ya kammala shirye-shirye don tabbatar da kammala daukar daliban aikin likitanci kamar yadda gwamnatin jihar ta umarta.
Alhaji Yahuza ya jaddada kudirin gwamnati mai ci a karkashin gwamna Bala Abdulkadir Mohammed, na inganta dukkanin sassan jihar gaba daya musamman bangaren lafiya ga ‘yan jihar.
Sanarwar ta ce, “Da wannan ci gaban, gwamna Bala ya nuna jajircewar gwamnatinsa na inganta fannin kiwon lafiya a jihar.”