A kwanan baya, yayin da firaministan kasar Girka Kyriakos Mitsotakis, ke ziyara a kasar Birtaniya, ya yi shirin ganawa da takwaransa na Birtaniya, Rishi Sunak, gami da tattaunawa tare da shi kan batun mayar wa kasar Girka da mutum-mutumin wurin ibada na Parthenon da gidan adana kayayyakin tarihi na kasar Birtaniya wato the British Museum ya mallaka. Sai dai, bayan da Mista Sunak ya ji yadda za a ambaci batun mayar da kayayyakin tarihi, nan take ya soke shirin ganawar, lamarin da ya fusata bangaren Girka sosai, har ma wasu kafofin watsa labaru na kasar Birtaniya su ma sun ce soke ganawar da Mista Sunak ya yi mataki maras ladabi ne. Sai dai a ganina, maimakon bayyana batun nan a matsayin wani mataki na maras ladabi da da’a, gara a ce Mista Sunak yana damuwa da jin tsoro. Kamar dai yadda Mitsotakis ya bayyana bayan abkuwar lamarin, inda ya ce “Duk wani dake da kwarin gwiwa kan gaskiyar matsayinsa, ba zai ji tsoron muhawara tare da saura fuska da fuska ba.” A zahiri dai, yadda Mista Sunak ya magance muhawara ya nuna ra’ayin gwamnatin kasar Birtaniya na damuwa kan yadda take mallakar kayayyakin tarihi na sauran kasashe daban daban.
Tabbas kasar Birtaniya za ta damu, saboda ta samu dimbin kayayyakin tarihi masu daraja da ake ajiyarsu cikin gidan adana kayayyakin tarihi na the British Museum ne, ta hanyar mulkin mallaka da wasoso a sauran kasashe. Kana a cikin kayayyakin da aka kwata, har da wasu kayayyakin tagulla fiye da 900 na kasar Najeriya. An bayyana sarai a shafin yanar gizo ko Internet na British Museum cewa sojojin kasar Birtaniya ne suka kwaci wadannan kayayyakin tagulla daga kasar Najeriya, lokacin da suka kai hari ga daular Benin a shekarar 1897. Saboda haka, cikin shekarun da suka gabata, kasashe da yawa da suka hada Girka, da Najeriya, da Habasha, da Masar, wadanda yawancinsu kasashe ne masu tasowa, sun yi ta kokarin matsawa gwamnatin kasar Birtaniya lamba, don ta mayar musu da kayayyakin tarihinsu.
- Jami’ar EDF: Matakan Lardin Guangdong Na Sin Kan Magance Sauyin Yanayi Abin Koyi Ne
- Shahararren Masanin Kasar Sin: Rasuwar Kissinger Ta Karfafa Gwiwar Bude Sabon Babi Ga Alakar Kasa Da Kasa
Sai dai, Birtaniya ba ta taba yarda da bukatar wadannan kasashe mai adalci ba, bisa dalilin wai dokarta ta hana a mayar da kayayyakin. A cewar kafofin watsa labaru na kasar Birtaniya, ainihin dalilin da ya sa kasar Birtaniya kin biyan bukatun wadannan kasashe, shi ne domin a ganinta, kasashen ba su da kwarewar da ake bukata a fannin kare kayayyakin tarihi. Dole ne a bar kayayyakin a hannun ’yan kasashen yammacin duniya, idan ana son kare su da nazari a kansu, saboda kasashen yamma cibiyar dan Adam ce ta kare al’adu da wayewar kai, wannan tunani ne na kasar Birtaniya, amma ko da gaske ne haka? A watan Agustan bana, wasu kayayyaki kimanin 2000 sun bace daga British Museum, inda har ma aka sayar da wasunsu ta shafin yanar gizo ko Internet, lamarin da ya nuna gazawar gwamnatin kasar Birtaniya a fannin kare kayayyakin tarihi.
Ko da yake ta kasa kare wadannan kayayyaki da kyau, amma duk da haka, gwamnatin kasar Birtaniya ta ci gaba da kin amincewa da mayar da su. Me ya sa take yin haka? A ganina, wasu mutanen Birtaniya na ci gaba da rike da tunanin “Kasancewar kasashen yamma cibiyar duiya”. Wato bayan da suka ga dimbin kayayyakin tarihi na kasashe daban daban da ake baje kolinsu cikin Museum din su, to, za su yi mafarki tamkar su ne suka gaji daukacin al’adun dan Adam, kana wai tarihi ya nuna cewa hanyar raya kasa ta kasashen yamma daidaitaciyar hanya ce daya tilo a duniya. Sa’an nan, lokacin da kasashe masu tasowa sun nemi a mayar musu da kayayyakinsu, mutanen Birtaniya za su ji tamkar ana neman farkar da su daga wani mafarki ne, amma fa ba su son farkewa. Saboda haka, sun fara magance tattaunawa, da damuwa a zuci, gami da rashin abin da ya kamata su yi.
Amma, tabbas ne za a farka, kome dadin mafarkin da ake yi. Wani yanayin da ake samu a duniyarmu shi ne, tasowar kasashe masu tasowa, da yadda aka fara samun wani tsari na kasancewar bangarori masu fada a ji da yawa a duniya. Kana a nasu bangare, kasashe masu tasowa ba za su taba daina kokarin neman dawo da kayayyakin tarihinsu ba. Saboda wadannan kayayyaki sun kunshi bayanan tarihin al’ummunsu. Dole ne a kare wadannan kayayyakin, da nazari a kansu yadda ake bukata, sa’an nan za a samu damar karfafa tunanin mutane na zama mambobin wata al’umma, da imani kan al’adun musamman nasu. Daga baya, za a iya daina kwaikwayon dabarun kasashen yamma, da kokarin nazari kan wata hanyar raya kasa, wadda ta dace da yanayin da kasar ke ciki, don neman raya kasa ta wata hanyar musamman da aka zaba da kai.
Idan an duba wani rahoton binciken sauraron ra’ayin jama’ar kasashe daban daban, da kafar watsa labarai ta CGTN na kasar Sin ya kaddamar, za a ga cewar, kashi 92.3% na dukkan mutanen da suka bayyana ra’ayoyinsu, sun yi kira ga gwamnatin kasar Birtaniya da ta sauke nauyin dake bisa wuyanta, sa’an nan ta mayar da martani ga bukatun kasashen masu tasowa, na komar da kayayyakin tarihi gidajensu. Saboda batun tasowar kasashe masu tasowa a bayyane yake, kana bukatarsu na da adalci. Shin kasar Birtaniya za ta iya ci gaba da magance muhawara, da kin daukar nauyi, har zuwa yaushe? (Bello Wang)