Gwamnatin Jihar Borno, ta bude sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi wanda zai zama mafaka ga wadanda mummunar ambaliyar ruwa ta shafa.
Da tsakar daren ranar Litinin zuwa wayewar Talata, mazauna birnin Maiduguri sun fuaskanci mummunar ambaliyar ruwa.
- Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Maiduguri
- Gwamna Uba Sani Zai Kaddamar Da Kwalejin Koyon Aikin Jinya Da Ungozoma A Pambegua
Lamarin ya faru ne bayan da wani sashe na madatsar ruwan Alau ya fashe ya haddasa kwarara ruwa zuwa unguwannin da ke kusa.
Wuraren da abin ya shafa sun hada da Shehuri, wasu sassa na Yankin G.R.A., Gambomi, Budum, Bulabulin, Adamkolo, Wurin Millionaires, Kasuwar Litinin da Gwange.
Cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun kakakinsa Bayo Onanuga, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa al’umar Borno kan wannan iftila’in.
“Shugaba Tinubu ya ba gwamnan Jihar Babagana Umara Zulum tabbacin cikakken goyon baya wajen tallafawa wadanda lamarin ya shafa.”
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya kai ziyara Maiduguri don jajanta wa al’uma, inda ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta yi gaggau5 ta mayar da mutane gidajensu.
Kuma tuni ya bai wa hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), umarnin kai dauki Maiduguri.
NEMA, ta ce tana aiki tare da hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), wajen samar da taimakon jin-kai ga wadanda ke cikin damuwa a sansanin.