Gwamnatin Jihar Edo ta yi Allah-wadai da kisan wasu matafiya ‘yan Arewa da aka yi a garin Uromi, da ke ƙaramar hukumar Esan ta Gabas, a ranar Alhamis.
Gwamna Monday Okpebholo ya ce za a binciki lamarin domin gano masu laifi da kuma hukunta su.
- Ribas: Ƙungiyar Ƙwadago Na Barazanar Shiga Yajin Aiki In Har Ba A Janye Dokar Ta-ɓaci Ba
- Kwankwaso Ya Yi Allah-wadai Da Kisan ‘Yan Arewa A Edo, Ya Buƙaci A Yi Adalci
Bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna wasu ‘yan banga suna tare matafiya ‘yan Arewa, suna fatattakarsu, sannan suka cinna musu wuta.
Ƙungiyar Amnesty International ta ce an kashe aƙalla mutum 16, ‘yan asalin Jihar Kano, waɗanda ke kan hanyarsu ta komawa gida don yin bukukuwan Sallah.
Gwamnatin Jihar Edo ta tabbatar da cewa ‘yan banga ne suka aikata harin.
Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Fred Itua, ya bayyana cewa waɗanda aka kashe sun fito daga Fatakwal, a Jihar Ribas, amma ‘yan banga sun ɗauka cewa ‘yan ta’adda ne.
Gwamna Okpebholo ya kai ziyara wajen da lamarin ya faru, inda ya jaddada cewa za a gudanar da bincike mai zurfi domin hukunta masu hannu a kisan.
Amnesty International da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, sun yi kira da a tabbatar da an yi adalci.
Gwamnan Edo ya yaba wa shugabannin Arewa bisa yadda suka kwantar da hankula tare da guje wa ɗaukar fansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp