Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya kafa wani kwamiti na musamman mai mutum 10 domin samar da hanyoyin magance matsalolin tsaro da suka addabi sassan jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, Samuel Jatau, ne ya bayyana haka a Jos ranar Alhamis, ya kuma bayyana cewa, kwamitin ya mai ritaya AVM Napoleon Bali ne zai jagorancin kwamitin a matsayin shugaba.
- Rikicin Filato: Atiku Ya Koka Kan Rashin Kwazon Jami’an Tsaro
- Ana Fargabar Kashe Mutane Da Dama Tare Da Kona Gidaje A Sabon Rikicin Filato
“Gwamnan ya amince amfani da kundin tsarin wannan kwamitin don tafiyar da al’amuran da suka shafi tsaro a jihar da kuma bayar da shawarwarin da suka dace ga gwamnati kan matakan da za ta dauka.
“Gwamnati za ta yi la’akari da kwarewar jami’anta, ko shakka babu cewa za su yi wannan aiki don amfanin jihar da kasa baki daya,” Cewar Jatau.
Mambobin kwamitin sun hada da Da Gyang Buba da Gbong Gwom Jos da Farfesa Ganyir Lombi da kuma Brig.-Gen. Gakji Shipi, mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin tsaro.
Sauran sun hada da mataimakan sufeto-janar na ‘yan sanda, Messrs Felix Vwamhi da Habila Jwalshak mai ritaya; Manjo Toholman Daffi mai ritaya kuma wakilin kungiyar nan ta Plateau Initiative for the Advancement of the Natives.
Ko’odineta na “Operation Rainbow“, rundunar tsaro ta jihar kuma memba, yayin da Jatau zai aiki a matsayin sakataren kwamitin.