Gwamnatin Jihar Filato za ta ba wa mata 1000 horo da sana’o’i daban-daban da suka hada da horar da su kan sanin makamar aiki don bunkasa tattalin arzikinsu da kuma sanya su zama masu dogaro da kansu.
Misis Helen Mutfwang, Uwargidan Gwamna Caleb Mutfwang na Filato, ta bayyana hakan a bikin ranar mata ta duniya a Jos.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Makiyayi Da Shanu 35 A Wani Sabon Harin A Filato
- Ana Kokarin Rantsar Da ‘Yan APC 16 A Majalisar Filato Ta Barauniyar Hanya – Gwamnatin Jihar
Misis Mutfwang ta ce, za a ba wa matan, musamman ma matasa horo na musamman kan fasahar zamani, kamar gyaran bidiyo da fina-finai.
Uwargidan gwamnan ta bayyana cewa jihar za ta kuma sanya wasu daga cikin matan a horar da su sana’ar kiwon kifi da sauran fannonin noma a jihar.
Ta bayyana cewa duk wadanda suka ci gajiyar shirin za a tallafa musu da tallafin fara sana’a a karshen horon.
Mutfwang ya ce taken ranar mata ta duniya ta bana, “Sanya hannun jari ga Mata.
Taken na nufin samar da wata duniyar jinsin mata ta musanman, da kuma jaddada bukatar kara saka hannun jari kan al’amuran mata don ba su damar samun damarmaki daban-daban don shiga cikin harkoki a dama da su.
“Ina kira ga matanmu da ‘yan matanmu da su yi amfani da wadannan damarmaki da gwamnatin Filato ta ba su domin kawo sauyi a jihar.
“Zan ci gaba da yin aiki tare da gwamnan don tallafa wa duk wani kokarin da ake yi na karfafawa da magance talauci, da kuma inganta karfin mata da ‘yan mata.
Misis Mutfwang ta kara da cewa, “Wannan shiri ne don ci gaban jihar.”