Gwamnatin Jihar Jigawa ta dage komawa makarantun sakandire da firamare da mako guda domin gudanar da aikin kidayar jama’a ta kasa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi da fasaha, Wasilu Umar Ringim ya raba wa manema labarai.
- ‘Yansanda Sun Kama Magoya Bayan Juventus 177 Saboda Kalaman Wariya
- Yawan Kudin Dake Shafar Tattalin Arzikin Yanar Gizo A Sin Ya Kai Matsayi Na Biyu A Duniya
Sanarwar ta ce an tsawaita wa’adin ne sakamakon aikin kidayar jama’a da za a fara a mako mai zuwa a fadin kasar nan.
A cewar sanarwar, “ma’aikatar ilimin kimiyya ta Jihar Jigawa tana son sanar da iyaye da shugabannin makarantun gwamnati da masu zaman kansu na jihar cewa an dage dawowa makarantu kamar yadda aka shirya a ranar Litinin mai zuwa 9 ga watan Mayu 2023.”
Ya ce ana sa ran daliban jeka ka dawo da n kwana za su kasance a makarantunsu a ranar Talata 9 ga watan Mayu 2023 domin fara darusan yau da kullum.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, an dauki matakin ne domin bai wa malamai da yara damar shiga da kuma kirga su a tsarin kidaya da za a yi.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su tabbatar da cewa yaransu sun koma makaranta a ranar da aka kayyade domin hukumomin makarantar ba za su amince da zuwa a makare ba ba tare da dalili ba.