Biyo bayan hadarin wani jirgin Kwale-Kwale da ya auku a ranar juma’ar da ta wuce, an sake gano gawarwakin Fasinjojin cikin jirgin hudu a yankin Mile 2 a jiya Asabar.
Jirgin wanda yayo jigilar fasinjojin 16 ya kefe ne a ranar daren juma’ar da ta wuce.
Janar Manaja na hukumar kula da rafukan jihar LASWA Mista Oluwadamilola Emmanuel ne ya tabbatar da sake gano gawarwakin ga kamfanin dillancin labarai na kasa a yau Lahadi,
Oluwadamilola ya ce, Gwamnatin jihar ta lashi Takobin kara daukar matakai don magance barin Ana yin amfani da kwale-kwalen da Ba sura ingancin safarar fasinjoji a jihar .
Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga ‘yan uwa da abokan arzikin wadanda iftila’in da rutsa da su.
Ya ce, a shekarun baya ne aka yanke wa wani direben Kwale-Kwale daurin rai da rai a gidan gyra hali saboda haddasa hadarin jirgin Kwale-Kwale a jihar.
Emmanuel ya kuma shawarci fasinjojin da ke hawan Kwale-Kwale a jihar da su tabbatar suna yin amfani da rigar kariya in sun hau Kwale-Kwale.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp